Gwamna Douye Diri na Jihar Bayelsa ya roƙi ‘yan Najeriya mazauna Amurka da sauran ƙasashen duniya su mara wa ƙasar su baya, duk kuwa da halin mawuyacin ƙalubalen da ta ke fama da shi.
“Ku yi haƙuri ku kawo ɗauki, kada ku bari ƙasar ku ta ruguje”. Haka Diri ya shaida wa ɗimbin mahalarta taron.
An shirya taron walimar cin abinci ne domin karrama gwamnan, wadda Jakadan Najeriya a New York ya shirya wa gwamnan a Ofishin Jakadancin Najeriya a New York, a ranar Laraba.
Diri ya ce matsalar tsaron da ake fama da ita a ƙasar, ana zuzuta ta ne kawai.
Diri ya ce Najeriya za ta ci gaba da bunƙasa sannu a hankali, kullum ta na ƙara ƙarfi a cikin gida da waje.
Diri ya ƙara da cewa duk da ana fama da gagarimar matsalar tsaro a wasu jihohi, to kuma akwai wasu jihohi da dama da ake zaman lafiya. Babu tashe-tashen hankula kuma babu zaman ɗar-ɗar, ko zaman zullumi.
“Jihar Bayelsa na sahun gaban jihohi waɗanda ke zaune lafiya ƙalau. Dalili kenan mu ka zo nan Amurka domin mu ka hankalin masu zuba jari su rungumi Jihar Bayelsa. Kuma za mu baje hajar kayan al’adun mu.
“Kamar yadda ku ka sani, a matsayin jihar Bayelsa mai albarkatun man fetur da gas, ganin yadda a yanzu duniya ke ƙoƙarin ganin an samu wanzuwar makamashi mai tsafta, to Bayelsa na da gas wanda ya ma fi fetur yawa.
“Mu na da albarkacin gas mai tarin yawa. Kai mun ma fi yawan gas fiye da ɗanyen mai. Saboda haka akwai damammaki masu yawa ga masu zuba jari a Jihar Bayelsa idan sun zo.” Inji Gwamnan.
Wani ƙarin albarkacin ƙasa a jihar Bayelsa kasr yadda Gwamna Diri ya fayyace wa mahalarta dinar, cewa ya yi baya ga ɗanyen mai da gas da Bayelsa ke tutiya da shi, akwai kuma albarkacin noma.
Ya ce gwamnatin jihar na zaburar da mutanen jihar su rungumi noma. “Saboda a jihar Bayelsa manomi zai iya noma shinkafa har sau uku a zagayen shekara ɗaya.”
Discussion about this post