Mataimakin takarar shugaban ƙasa na Peter Obi a jam’iyyar LP Doyin Okupe, ya bayyana cewa Obi zai bayyana takamaimen ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa kafin ranar Juma’a.
Okupe wanda ke riƙe da matsayin na je-ka-na-yi-ka, kafin a naɗa takamaimen ɗan takara, ya ce Obi da LP za su bayyana ɗan takarar mataimaki biyo bayan rugujewar ƙawancen da LP da kuma NNPP ta su Rabiu Kwankwaso.
Okupe ya ce tun kimanin makonni huɗu da su ka gabata ƙawancen da aka yi ƙoƙarin ƙullawa tsakanin LP da NNPP ya kakare.
Don haka a wata hira da Okupe ya yi da gidan talabijin na Channels a ranar Talata, ya ce Obi zai bayyana ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, kuma daga Arewa zai fito.
“Zai ɗauko ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na LP daga Arewa, kuma za a ɗora masa nauyin shiga da nausawa cikin Arewa ya na tallata jam’iyyar domin ta samu tagomashi a Arewa.”
Tun cikin watan Yuni Okupe ya ce zai kasance ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na LP, amma na riƙo kafin a ɗauki mataimaki daga Arewa.
Da ya ke magana kan haɗewar Obi da Kwankwaso, Okupe ya ce tunin lamarin ya kakare, kawai yanzu kowa ya je ta sa ta fisshe shi.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin da makusantan Kwankwaso su ka ce ba zai yi wa Obi mataimaki ba, saboda ya fi shi jama’a, sai dai Obi ya zama mataimakin Kwankwaso.
Discussion about this post