Kotun Sauraren Ƙararrakin Bin Haƙƙin Ma’aikata a Abuja, ta umarci Gwamnatin Tarayya ta ƙara wa Cif Jojin Najeriya da sauran alƙalai kakaf albashi da alawus-alawus.
Mai Shari’a Osatohanmwen Obaseki ne ya zartas da hukuncin a ranar Laraba, inda a yayin yanke hukuncin ya ce “albashin da ake biyan alƙalai a Najeriya abin kunya ne.”
Ƙarin albashin dai ya biyo bayan wata ƙasa da Babban Lauya Sebastine Hon ya shigar, inda ya nemi cewa Najeriya ta tauye wa alkalai haƙƙin su na albashin da su ka cancanci su riƙa karɓa.
Ya nuna wa kotu cewa rabon da a yi wa alƙalai ƙarin albashi tun cikin 2008.
A ƙarar dai Obaseki ya nemi kotu ta tilasta wa Majalisar Dattawa, Antoni Janar kuma Ministan Shari’a da Hukumar Rarraba Kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya su ƙara wa alƙalan Najeriya albashi.
Idan ba a manta ba, cikin watan Yuni ne Babban Mai Shari’a na Kotun Ɗaukaka Ƙara ya yi roƙon a ƙara wa alkalai albashi.
Shugaban Kotun Ɗaukaka Ƙara ya roƙi Gwamnantin Tarayya ta ƙara wa alƙalai albashi.
Ya ce rabon da a yi masu ƙarin albashi tun cikin 2008, lokacin dala ɗaya ba ta kai Naira 120 ba.
Bayan Lauya ya shigar da ƙarar neman ƙarin albashi ne kuma sai Ministan Shari’a da Majalisar Dattawa su ka nemi kada kotu ta ƙara wa alƙalai albashi.
Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya, Monica Dongban-Mensem, ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi wa alƙalai ƙarin albashi.
Monica wadda ta yi roƙon a yi ƙarin albashin, ta yi roƙo a wurin ƙaddamar da taron shekara na Kotun Ɗaukaka Ƙara na farko na 2021/2022, a Abuja a ranar Litinin, ta ce rabon da a yi wa alƙalai ƙarin albashi tun cikin 2007.
Ta nuna damuwa ganin yadda za a ce ana biyan Babban Jojin Najeriya (CJN) Naira 279,497 a matsayin albashin wata-wata. Yayin da manyan alƙalan Kotun Ƙoli ake biyan su Naira 206,425 kacal su ma.
Monica ta ce a matsayin ta na Babbar Mai Shari’a kuma Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara, Naira 206,425 ake biyan ta albashin wata-wata. Yayin da Alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙara ake biyan su Naira 166,285.
Yayin da ta ke kwatance tare da suna albashin su da na Alƙalan wasu ƙasashe, Monica ta ce albashin da ake biyan Alƙalan Najeriya cikin cokali ne, idan aka auna shi kan sikeli ɗaya da na wasu ƙasashe, har da wasu masu maƙwautaka da Najeriya.
Daga nan kuma ta yi kira ga gwamnatin tarayya da na jihohi su riƙe alƙawarin barin alƙalai da Majalisun Dokokin Jihohi su ci gashin kan su, kamar yadda Dokar Musamman ta 10 ta 2020 ta amince.
“Kusan shekaru sama da 10 kenan rabon da a yi mana ƙarin albashi.” Inji Monica, kuma ina roƙon a ƙara wa Kotun Ɗaukaka kuɗaɗen da ake bata, domin muna so mu fito da tsarin ingantawa da kirƙiro matakan sauƙaƙa batutuwa na yanke hukunci.” Inji Monica.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin da Malami da Majalisar Dattawa su ka nemi kada a ƙara wa alƙalai albashi.
Majalisa da Malami sun soki ƙarar neman a ƙara wa alƙalai albashi.
Kotun Shari’ar Haƙƙin Ma’aikata ta aza ranar 15 Ga Yuli domin yanke hukunci kan shari’ar da ake tafkawa ta neman a ƙara wa alkalan Najeriya albashi da alawus.
Mai Shari’a Osatohanmwen Obaseki ne ya aza ranar yanke hukuncin, bayan da lauyoyin ɓangarorin biyu kowane ya shaida wa kotu cewa ya gama gabatar da bayanai da hujjoji da shaidun sa.
Lauya Awomolo Adegboyega wanda ke wakiltar wanda ya shigar da ƙara, ya shaida wa kotu cewa masifar tsadar rayuwar da ake ciki a ƙasar nan ta sa tilas fa sai an duba albashin masu shari’a an yi masu ƙari.
Awomolo wanda babban lauya (SAN) ne, ya bijiro da matakai huɗu a kotu, kuma ya roƙi duk a biya masa buƙatar su.
Wani mai suna Sebastine Hon ne dai ya shigar da ƙarar.