Kotu a Tsafe jihar Zamfara ta dage cigaba da shari’ar wani mutum mai suna Musa Tsafe da ya auri jikar sa shekaru 23 da suka wuce.
Hukumar Hisbah ta jihar Zamfar ce ta shigar da ƙara kotu inda ta bayyana cewa abinda Musa yayi ya saɓa wa karantarwar addinin musulunci.
Musa ya ce yana son matan sa wacce jikar sa ce mai suna Wasila, kuma ba zai sake ta ba.
Rahotanni daga kotun da aka saurari wannan kara sun nuna cewa ba tun yanzu bane aka yi ta kai ruwa rana da Musa kan rashin halascin auran jikar sa da yayi shekaru 23 da suka wuce amma ya ki sauraren kowa.
Tsakanin sa da Wasila suna da ƴaƴa 8 kuma ya lashi takobin sai ya ga abin da ya ture wa buzu naɗi game da hakan domin bazai saki Wasila ba.
Kotu ta ɗage shari’arzuwa ranar 25 ga wata domin cigaba da shari’ar