Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyyar LP, Peter Obi, ya bayyana cewa duk da LP ba ta samu ƙuri’a ko kashi 1% a zaɓen Osun ba, an yi gumurzun zaɓen gwamnan Jihar Osun da su sosai.
A ranar Lahadi ce Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC ta bayyana cewa Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ne ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Osun, wanda aka yi a ranar Asabar.
Adeleke ya samu ƙuri’a 403,371, shi kuma Gwamna Adegboyega Olusola na APC ya samu 375,027.
Yusuf Lasun ne ɗan takarar LP, wanda ya samu ƙuri’u 2,729, wato kusan kashi 0.34 kenan na yawan ƙuri’un da aka jefa.
Amma duk da haka Peter Obi ya ce LP ta yi ƙoƙari sosai a wurin zaɓen.
“Ina taya ɗan takarar LP, Lasun Sulaiman Yusuf murnar fafata gumurzun zaɓen gwamnan Jihar Osun, kuma ina taya mataimakin takarar sa murna, wato Adeola Adekunle Atanda. Sun shiga fagen daga, an kafsa da su kuma sun yi jarunta, duk kuwa da cewa ga yadda sakamakon zaɓen ya kasance.” Haka Obi ya ributa a shafin sa na twita ranar Lahadi.
“Rashin nasarar da LP ta yi a zaɓen gwamnan Jihar Osun, ba ya na nuni da yadda zaɓen shugaban ƙasa zai kasance ba a zaɓen shugaban ƙasa”.
Ya ce LP za ta bada mamaki sosai a zaɓen shugaban ƙasa nan da 2023.
Obi ya ce tunda dai bai fi wata ɗaya da shiga cikin LP ba, to sakamakon zaɓen kwanan nan kada ma ya tayar da hankalin ɗimbin magoya bayan sa, domin waɗanda su ka yi nasara da sauran waɗanda ake gogayya da su, tsoffin ‘yan alewa ne a siyasar ko a zaɓen.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga yadda gwanin rawa, Sanata Adeleke, kawun Davido ya farfasa gangunan Buhari, Tinubu, APC da Oyetola ya lashe zaɓen gwamna.
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta bayyana Ademola Adeleke na PDP cewa ya yi nasara a zaɓen gwamnan Jihar Osun.
Da ya ke sanarwar a safiyar Lahadi, Baturen Zaɓe na Jihar Osun Oluwatoyin Ogundipe, ya bayyana cewa, “Ademola Adeleke na PDP ya samu ƙuri’u 403, 371. Shi kuma Gwamna Gboyega Oyinlola ya samu 375, 027.”
“Saboda ka samu yawan waɗannan ƙuri’u, to ka cika sharuɗɗan cin zaɓe. Don haka kai ne ka yi nasarar zaɓen gwamnan jihar Osun, wanda aka yi ranar Asabar, 16 Ga Yuli, 2018.
Baya ga lashe zaɓen, Adeleke ya yi nasara a Ƙananan Hukumomi 17 daga cikin 30 da ke jihar. APC ta samu ƙananan hukumomi 13.
Sauran jam’iyyu 13 kuwa babu wadda ta samu ko ƙaramar hukuma ɗaya.
Ramuwar Gayyar Kwankwatsar Da Su Tinubu Su Ka Yi Wa Adeleke A 2018:
Zaɓen gwamnan Osun rayuwar gayya ce Adeleke ya yi kan Oyetola, Tinubu da Shugaba Muhammadu Buhari, da kuma APC kacokan.
A zaɓen 2018, APC ta cika Osun da gwamnoni da jiga-jigai, inda aka kayar da Adeleke na PDP, bayan an yi zaɓen ‘inkwankilusib’.
An yi wa Adeleke taron dangi, inda har aka haɗa da wasu jam’iyyu, domin a kayar da Adeleke a wata rumfar zaɓe ɗaya tal.
Zaɓen yanzu na 2022 kuwa alama ce mai nuna cewa ɗan takarar APC a zaɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu zai sha wahala a yankin sa na Kudu maso Yamma. Tunanin da ake yi cewa zai kwashi miliyoyin ƙuri’u a ɓagas, zaɓen Osun ya nuna ba haka siyasar za ta kasance ba.
Mulkin Adeleke zai fara ne daga watan Nuwamba, sadda wa’adin gwamnan da ya sha kaye zai ƙare.
Zaɓen ya ƙara zama tarihin da ɗan takara ya kayar da gwamna wanda ke kan mulki, kuma wanda jam’iyyar sa APC ke mulki a ƙasa.
PDP ta ƙwace jihar Osun, makonni uku bayan ta kasa ƙwato jihar Ekiti daga APC.
Discussion about this post