Kamfanin mai na kasa mai zaman kansa ya karyata rahotannin da suka karade kafafen yada labarai cewa wai ya sallami daruruwan ma’aikatan kamfanin.
Kamfanin ya ce bai sallama ba kuma ba bu shirin yin hakan nan kusa.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabon kamfanin mai na NNPC, wanda a yanzu zai riƙa aiki tamkar kamfanoni masu zaman kan su, ba na gwamnati ba.
Da ya ke ƙaddamar da sabon NNPC ɗin, Shugaba Muhammadu ya ce ana sa ran daga yanzu kamfanin zai riƙa gudanar da ayyukan sa kuma a riƙa tafiyar da shi kamar yadda ake gudanarwa ko tafiyar da duk wani kamfanin ‘yan kasuwa masu zaman kan su.
Hakan ya na nufin za a daina bin hanyar da ake tafiyar da NNPC, inda aka maida shi saniyar tatsar da nonon da ba ya ƙarewa.
Sabon kamfanin NNPC ɗin dai a yanzu tuni masu hannayen jari sun sayi hannaye miliyan 200.
Buhari ya ƙaddamar da shi ne a Fadar Shugaban Ƙasa, ranar Talata a Abuja.
“A yau mu na sauya wa kamfanin mu na harkokin fetur alƙibla, daga yau 19 Ga Yuli, 2022.” Inji Buhari a wurin taron.
“A yanzu NNPC zai riƙa aiki a matsayin kamfani mai zaman kansa wanda áƙalla ‘yan kasuwa ke da hannayen jari miliyan 200 a cikin sa.
An buɗe kamfanin makonni da dama bayan aka maida hukumar NNPC ta zama kamfani wanda dukkan ayyukan sa zai yi sai a ƙarƙashin Dokar Kafa Kamfanoni ta Kasa (CAMA), wadda aka ƙirƙiro domin a halasta Sabuwar Dokar Fetur, wadda ta fara aiki a ranar 1 Ga Yuli.
Tun a cikin Satumba aka kammala sauya NNPC zuwa kamfani mai zaman kan sa, bayan da Shugaban Ƙasa ya sa wa Sabuwar Dokar Fetur (PIB), ta tashi daga ƙudiri (PIB) ta koma doka (PIA).
Daga nan aka narka masa jarin kasuwanci na Naira biliyan 200.
Daga yanzu ana sa ran NNPC zai riƙa samar wa kan sa riba kamar sauran kamfanoni, ba tare da sa hannun gwamnati ba.
Discussion about this post