Hikayata gasa ce ta ƙagaggun gajerun labarai wadda ke samar da dama ga mata marubuta, waɗanda ba su ƙware ba da kuma ƙwararru don nuna fasaharsu da ba da damar karanta labaransu a harshen Hausa.
Dole ne labaran da za a shiga su kasance ƙagaggun labarai kan wani jigo.
Mata biyu na iya haɗa gwiwa su shigar da labari guda amma ka da su haura mata biyu, kuma labari ɗaya kacal mace za ta iya shigarwa.
Gasar dai ta mata zalla ce wadanda shekarunsu ba su gaza 18 ba sannan kuma ba su wuce 35 ba.
Za a rufe gasar da karfe 23:59 na ranar 31 ga watan Yulin 2022.
Ku tabbatar kun karanta ka’idojin gasar da dokokin bayanan sirri na BBC kafin ku shiga gasar: Yadda za a shiga gasar
Discussion about this post