Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya na farin ciki da alfahari zai sauka cikin 2023, zai bar kyakkyawan tarihin daƙile rashawa da cin hanci.
Ya yi alƙawarin ci gaba da goyon bayan duk wani ƙoƙarin kakkaɓe rashawa da cin hanci a Najeriya da Afrika baki ɗaya, ko ya na mulki ko bayan saukar sa.
Buhari wanda ya hau mulki a ƙarƙashin APC cikin 2015, ya yi alƙawarin ci gaba da yaƙi da rashawa da cin hanci, inganta tattalin arziki da kuma kare al’ummar ƙasar nan daga matsalar tsaro, zai kammala wa’adin mulkin sa bayan zaɓen 2023.
Ya yi jawabi ne a wani faifan da aka ɗauki muryar sa aka kunna a wurin taron da Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (PACAC) ya shirya tare da haɗin guiwar EFCC da ICPC, ranar Alhamis a Abuja.
An shirya taron ne domin tattauna darasin da aka koya wajen yadda aka yi aiki da Kuɗaɗen Tallafin Korona.
Buhari wanda zai sauka daga mulki kafin nan da shekara ɗaya, ya jaddada rashin ƙaunar da ya ke wa rashawa da cin hanci, tare nanata aniyar sa ta kakkaɓe rashawa da cin hanci a Najeriya.
Ya ƙara tinƙaho da dukan ƙirji tare da nasarorin daƙile rashawa da cin hanci da ya ce gwamnatin sa ta yi daga 2015 zuwa yau.
“Zan bar ofis cikin shekara mai zuwa, ina mai cike da alƙawarin zan sauka cikin farin cikin harin kyakkyawan tarihin daƙile cin hanci da rashawa, daga cikin nasarorin da na samu.”
Ya ce “idan aka kashe cin hanci da rashawa a Najeriya da Afrika baki ɗaya, to za a samar wa ‘yan ƙasa kyakkwar rayuwa kenan.”
Yayin da ya ke cewa yaƙi da rashawa da cin hanci ba abu ne mai sauƙi ba, ya ƙara da bayar da hasken cewa akwai sauran aiki wajen ƙwato kadarori daga hannun ɓarayin gwamnati, a fannin gurfanar da ɓarayin gwamnati a kotu, wajen yanke masu hukunci, matakan kama su da ma wajen batun dokokin da su ka shafi yaƙi da cin hanci da rashawa ɗin baki ɗaya.
Discussion about this post