Koda yake jihar Kaduna ta kusa zama Landan din Arewa dubi da irin ayyukan da cigaba da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya jijjibga a kamar babu gobe. Wannan shine babban dalilin da ya sa mutan Kaduna suka fara kewar sa tun kafin wa’adin sa ya ciki.
Idan dai ba batulci ba, a jihar Kaduna, idan baka yabi Nasir El-Rufai ba, ba ka ko zage shi idan cigaba kake so ko muradi a duk inda kake musamman idan kai mazaunin jihar Kaduna ne.
Wani abin yayi na girma da dattaku shine, zaɓin sanata Uba Sani da yayi wanda zai gaje shi. Duk da dai za aiya cewa mutum tara yake bai cika goma ba kamar yadda Hausawa ke cewa, ga dukkan alamu gwamna El-Rufai ya yi wa mutan Kaduna kyakkyawar zaɓi da mutum nagari, mai kishi da son talakawa.
Na gamu da wata dattijiya a garin Kaduna wanda ta ce a garin aka haife ta amma zata iya rantsewa da za a gaya mata irin ayyukan da gwamnatin El-Rufai ta yi zai yiwu da ba zata yarda ba.
” Na ji da kunne na yadda mutane musamman marasa galihu da ƴaƴan talakawa ke kwarara wa Uba Sani addu’o’i a wurare da dama a garin Kaduna, kuma basu ma san shi ba.” In ji Dattijiya Abu.
Idan mutane za su yi nazari mai zurfi za su ga cewa Uba Sani mutum ne wanda shi neman yadda zai taimaki mutane yake yi. Bin inda suke yake yi yana musu alkhairi. Gwamnatin sa a jihar Kaduna za ta inganta rayuka da kuma jawo talaka kusa da gwamnati, saboda ita Juma’a mai kyau tun daga Laraba ake gane ta. Tun yanzu Mutan Kaduna sun gane cewa ‘dame ne suka tsinta a kale’, fitowar sanata Uba takarar gwamnan jihar.
Uba Sani yana da gaskiyar da bai tunanin akwai wanda zai iya saka shi ya kauce hanya saboda son rai da nukufarci. Idan ya fuskanci gabas gabas ɗin nan ya nufa, kuma xan za shi sai an ce masa ya isa haka.
Ni dai mai wannan rubutu na gani kuma naji daga mutanen Kaduna cewa akwai alkhairi tattare da Uba Sani. Ba musulmai ba ba ga Kiristoci, Kudqncin Kaduna da Arewacin Kaduna duk suna tare da sanata Uba.
Mutan Kaduna sai sam barka.
Daga Mohammed Ibn Mohammed
Discussion about this post