Bayan godiya ga Allah(swt) da salati ga manzon tsira (saw).
ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR,LAA ILAAHA ILLALLAH, WALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR WA LILLAHIL HAMD*
Yaku ‘yan uwa musulmi!Kuji tsoron Allah madaukaki ku tina falalar da Yayi muku na Bikin Sallar idi Babba, Biki ne da zukata suke cike da farinciki da murna. Ranar da musulmi suke fita Sallar Idi, suna masu godiya da kabarbari suna godiya ga ni’imar da Allah Ya yi agare su.
#Yaku ‘yan uwa!Musulunci ya haramta zudda jini da cin dukiya ta hanyar da bata dace ba, da kuma keta mutuncin, Haramci na har Abada.
An karbo daga Abu Bakr(R.A) daga Manzon tsira SAW, Yace: “lallai jinanenku, dukiyoyinku da mutuncin ku haramun ne akan ku, kamar alfarmar Wannan rana ta Arafah, alfarmar Wannan gari naku (Makkah), da Kuma alfarmar Wannan wata naku (dhul-hijjah)…Kuma hakika zaku hadu da Ubangijin ku, zai tambaye ku game da ayyukan ku”.
ya ku ‘yan uwa! Mu sani dukkanin musibu da fitintinu da rashin tsaro da fatara da muka shiga yau ta dalilin muyagun ayyukan mu ne da muke aikatawa a bayan kasa, don haka mu nisanci su. (Al-ayah..41-Ruum).
A wannan zamani sabbin hanyoyin yada alfahsha, fasadi, izgilanci, almundahana da makamantansu sun bayyana, kuma Allah SWT yayi hani game da haka. (Ayah..19-Nuur). Ku sani cewa ayyukan zunubi suna haifar da illoli da sharrori masu girman gaske a rayuwar ku da tattalin arzikinku da lahiranku.
Yaku iyaye Mata! Kuji tsoron Allah ku kiyaye dokokinsa, Kuma ku nisanci abin da yayi hani da shi kuma ya tsawatar, Kuma kuyi biyyaya ga mazajenku kuyi tarbiyyar ‘yan’yanku. Ku nisanci shirka da bayyana tsiraicinku. Domin ya inganta daga Manzon tsira SAW, yayinda ya wuce mata a wurin sallar idi yace: “ya ku mata! Ku ringa sadaka, domin lallai naga mafiya yawanku a cikin wuta”.
Yaku musulmi! Lallai jagorancin al’umma (Siyasa) al’amari ne na wajibi a addini, matukar al’umma na son ci gaba.. domin Manzon tsira SAW ya umurce ku da sanya shugaba da yi masa biyayya.
A karshe ‘yan uwa! Muyi siyasa mai tsafta domin samun maslaha ba fitina ba.
Allah madaukaki ya kare mana imanin mu da mutuncin mu.
Discussion about this post