Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa gwamnatin Muhammadu Buhari mai mulki ta ci amanar ƴan Najeriya a tsawon mulkinta a ƙasar nan.
Kakakin jam’iyyar Debo Ologunagba ya bayyana cewa ” Irin mulkin kama karyar da APC ta ke yi a kasar nan da kuma nuna halin ko in kula da ta ke yi kan kiyaye rayukan mutanen kasar ya nuna gazawar gwamnatin.
” Ku duba yadda ƴan bindiga suke cin karen su ba babbaka a kasar nan. Duk wanda ya ga yadda ƴan bindiga ke jibgar mutanen da basu ji ba basu gani ba sannan kuma gwamnati ta zuba musa ido, ina talaka zai saka kansa?.
” Karkashin wannan mulki na APC, kisa ya zama kusan jiki ga mutane. Gaba ɗaya jam’iyyar ta ruguza tsarin zaman lafiya a ƙasar wanda talakawa suka saba da ita. Abu kamar wasa, kirikiri abu ya zama ruwan dare ta ko ina kisa kawai ake yi sannan babu wani abu da gwamnati ke iya yi.
” Daga 2020 zuwa yanzu ƴan bindiga sun kashe mutum sama da 18,000. Kuma wai ace akwai gwamnati a kasar nan. Komai ya daburce, talaka ya afka cukin ruɗani, babu inda zai saka kansa amma kuma kullum sai kurin gwamnati ta kusa gamawa da su, amma jiya iyau.
A ranar Litinin ƴan bindiga sun saki ƙarin wasu fasinjoji 3 daga cikin fasinjojin da ƴan bindiga suka sace a layin jirgin kasa daga Abuja-Kaduna.