Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya bayyana cewa har yau gwamnati ba ta samu mafita daga matsalar da ta dabaibaye harkokin jiragen sa ba a Najeriya.
Da ya ke magana a taron da ya yi ranar Talata da Ƙungiyar Masu Safarar Jiragen Sama ta Ƙasa (AON), Sirika ya ce ƙarancin mai da jiragen sufuri ke fama da shi, ba a Najeriya kaɗai ba ne. “Matsalar ta shafi duniya, tun daga Amurka har Newzealand.
“To mu a nan Najeriya lamarin ya fi muni ne saboda ba mu tace man a cikin gida.”
Wata matsalar a cewar Sirika ita ce ƙarancin dala da kuma karyewar darajar naira a kasuwar hada-hadar canji.
Ya ce a ƙoƙarin da gwamnati ke yi shi ne ƙoƙarta ganin an gyara wasu matatun mai domin a samu sauƙin samun man.
Haka dai Sirika ya ce kuma ya ƙara da cewa babban abin da Najeriya ke jira shi ne a ga matatar man Ɗangote ta fara aikin tace mai.
“A yanzu dai gaskiya babu wata mafita. Sai fa ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen shigo da ɗan wanda ya sauƙaƙa.
“Sai dai mu jira lokacin da aka fara tace mai a Matatar Ɗangote. Ban san rana ko lokacin da za a fara tace man ba.”
Matsalar mai ta sa masu kamfanonin jiragen sama ƙara kuɗin tikiti zuwa Naira 50,000 abinda ya yi sama. Sai dai kuma hakan bai magance matsalar ba.
Da ya ke jawabi, Shugaban Ƙungiyar Masu Jiragen Sama, Abdulmunaf Sarina, ya ce sun fara shiga wannan matsala ce tun da litar man jirage ta fara tashi, inda farashin ya riƙa tashi daga naira 180 har sai da ya dangana Naira 1,000.
Tuni dai wasu kamfanonin jiragen su ka dakatar da zirga-zirgar jirage a ƙasar nan.
Discussion about this post