Mazauna kasuwar Sansanin Alhazan Kano da sauran masu hada-hada a Kasuwar Hajji Camp a Kano, sun cika da mamakin ganin yadda wani magidanci ya fara ‘aikin Hajjin sa’ a ranar Alhamis, a Sansanin Alhazan Kano.
Jibrin Abdu na cikin maniyyata fiye da 1,500 waɗanda aka yi masu sakacin kasa kwasar su zuwa Saudi Arabiya, domin aikin Hajjin 2022.
Jibrin ya shaida wa manema labarai cewa ya ya fara aikin Hajji a cikin sansanin tun a ranar Alhamis.
“Na yi Safa da Marwa, kuma na yi Sallah a Maƙama Ibrahim da ke ɗakin Ka’aba.
Jibrin ya yi amfani da kwaikwayon ginin Ka’aba da aka yi a Sansanin Alhazan Kano, a matsayin Ka’abar sa. Kuma a cikin sansanin ya yi ‘Safa da Marwa’.
Ya bayyana cewa saura ɗawafi da jifar Shaiɗan ya rage masa.
Ya nuna takaicin yadda aka bar su a baya, alhali ya biya Naira 2,500,000 cif.
Sannan kuma ya ce duk mai hannu wajen haddasa barin su a baya, to ya bar su da Allah kawai.
Tuni dai Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta bayar da haƙuri ga maniyyata sama da 1,500 da ba a samu damar kwashewa ba.
Daga cikin waɗanda ba su samu damar tafiya ba, akwai maniyyata 700 daga Kano, 750 ‘yan jirgin-yawo, watau ‘International Travellers’, 91 daga Filato sai kuma 9 daga Bauchi.
Jibrin Abdu wanda ya ce daga Ƙaramar Hukumar Gezawa a Kano ya ke, ya ce ya na kyautata zaton Allah zai karɓi ibadar sa, saboda niyyar sa zai duba. A cewar sa, “ai ko’ina akwai Allah.”
Ya ce ya na da mata huɗu da ‘ya’ya 26.
A ƙarshe ya bugi ƙirjin cewa, “duk duniya babu mai bin sa bashi, sai matar sa uwargida mai bin sa bashin naira 30.
Discussion about this post