Mataimakin takarar Bola Tinubu a jam’iyyar APC, Kashim Shettima, ya shaida wa Shugaba Muhammadu Buhari cewa Gwamnonin Najeriya na ƙarƙashin APC sun so a bai wa Gwamna Babagana Zulum takarar mataimakin shugaban ƙasa.
Shettima ya shaida wa Buhari haka, jim kaɗan bayan da Tinubu ya ƙaddamar da shi a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Shettima ya je Fadar shugaban Kasa ne domin nuna godiya bisa goyon bayan da aka ba shi har aka tsayar da shi mataimakin takarar shugaban ƙasa.
Shettima wanda ya kai ziyarar tare da Gwamna Zulum da Ƙaramin Ministan Gona, Shareku, ya shaida wa Buhari irin yadda gwamnonin APC su ka riƙa matsa wa Zulum lallai ya amince a tsayar da shi mataimakin takara, amma ya ce a’a.
Daga nan ya jinjina wa Zulum sosai ganin yadda ya zaɓi ci gaba da mulki a jihar Barno, maimakon ya tafi takarar mataimakin shugaban ƙasa.
Kafin nan dai Shettima ya jinjina wa Buhari tare da yi masa godiya kan irin ayyukan raya jiha da jihar Barno ta samu a zamanin mulkin APC.
Shugaba Buhari shi ma ya ce “zaɓen Kashim Shettima a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa abu ne mai kyau ƙwarai, saboda ya cancanta.
Ya ce Shettima ya yi Gwamna shekara takwas, kuma ya na sanata, duk tsawon shekarun kuma ya na taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa APC.
Buhari ya ƙara jinjina wa Shettima, ganin duk da cewa a yanzu ba shi ne Gwamna ba, amma bai yada mutanen karkara da jihar sa baki ɗaya, kuma ya na tare da gwamnan da ya gaje shi.
Buhari ya jaddada wa Shettima cewa APC ce za ta yi nasara a zaɓen 2023, kuma kai da Tinubu zan miƙa wa mulki.
“Sai dai kuma maganganu na yabo da ka yi min, zan ƙyale ka, ba zan ba ka amsa har ranar da na miƙa maku mulki kai da ogan ka Tinubu tukunna.” Inji Buhari.