Gwamnatin Zamfara ta dakatar da Yandoton Daji, Aliyu Marafa, wanda ya nada Ada Aleru kasurgumin ɗan bindiga sarauta.
An nada Aleru Sarkin Fulanin yankin Yandoto.
Sakataren masarautar ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa an nada Aleru sarautar sarkin Fulani domin a samu zaman lafiya a yankin karamar hukumar Tsafe, jihar Zamfara.
Bayan haka gwamnati ta kafa kwamiti domin binciken musabbin abin da ya faru da ya kaiga har ana yi wa kasurgumin ɗan bindiga sarauta, bayan gallaza wa mutane azaba da ya yi da kisa ba adadi.
Masarautar ‘Yandoton Daji na ɗaya daga cikin sabbin masarautu biyu da Gwamnatin Zamfara ta ƙirƙiro cikin watan Mayu. An ciri masarautar daga Masarautar Tsafe. Aliyu Marafa ne aka naɗa Sarkin ‘Yandoton Daji.
An amince a naɗa wa gogarma Aleru sarautar Sarkin Fulanin ‘Yandoton Daji tsakanin su dattawan masarautar da kuma amincewar shi Aleru ɗin.
Cikin watan Maris PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa a lokacin da aka yi zaman neman sasantawa a samu zaman lafiya a cikin Maris, dattawan yankin sun roƙi Aleru ya daina kai hare-hare a masarautar.
“Aleru ya tara maƙudan kuɗaɗe da shanu masu yawan gaske. To kuma ya na sane da cewa idan ya ci gaba da yaƙi da sojojin Najeriya, to ko ba-jima ko ba-daɗe zai yi asarar shanun sa da dukiyar sa suka. A matsayin sa na shugaban ‘yan bindigar yankin ‘Yankuzo da Munhaye da kewayen yankin, ya na ganin abu mafi muhimmanci a gare shi, shi ne yin sulhu kawai.” Haka wata majiya ta shaida wa wakilin mu.
Wata majiyar kuma wadda ma’aikacin gwamnati ne a Tsafe, ya sanar da wakilin mu cewa an yanke shawarar naɗa Aleru sarautar Sarkin Fulani domin a nuna masa godiyar zaman lafiyar da aka samu na raguwar kai hare-hare a yankin.
“An yi wani taro makonni biyu da su ka wuce, waɗanda su ka halarci zaman sun gamsu da ƙoƙarin da Aleru ya yi na daina kai hare-hare a yankin. Bai roƙi a ba shi sarauta ba. Masarautar ce ta yi amanna da cewa idan aka naɗa shi Sarkin Fulani, to za a huta da fitinar sa shi da yaran sa masu yawa.”
Bayyanar Gogarma Ada Aleru Da Iyalin Sa A Sallar Idi A Tsafe:
Majiya ta shaida wa wakilin mu cewa Ada Aleru ya je Sallar Idi a cikin dandazon mutanen gari, a Tsafe, a ranar Asabar. Wannan lamari dai mutane da dama na yi masa kallon cewa alama ce mai nuna Ada ya karɓi tayin zaman lafiyar da aka yi masa.
“Ni na je Sallar Idi, na kuma ga lokacin da Aleru ya je shi da wasu yaran sa da iyalin sa. Kuma dukkan su babu mai riƙe da bindiga.” Haka wannan ma’aikacin gwamnatin ya shaida wa PREMIUM TIMES.
Ma’aikacin ya kuma bada dalilin sa na goyon bayan bai wa Aleru sarautar da ake shirin yi a ranar Asabar.
“Shin yaushe rabon da mu kira ka mu sanar da kai cewa an kai hari a Tsafe da kewaye? Ni na san wasu mutane ba za su yi murna ba, za su ji haushi, rayukan su zai ɓaci. To amma abin tambaya shi ne, ko gwamnati za ta iya yin nasara a kan ‘yan bindiga ne?”
Ya ƙara Aleru zai je tare da sauran riƙaƙƙun ‘yan bindiga, irin su Ali Zakwai, Bello Kachalla Turji, Yellow Ɗanbokolo, Sanata, Isuhu Yelo, Damina da Mai Shamuwa.
“Mu mun yi amanna cewa Aleru zai haɗa kan waɗannan riƙaƙƙun ‘yan ta’addar su zo a zauna domin a samu zaman lafiya.” Haka wata majiya a fadar Sarki ta sanar wa wakilin mu.
An tambaye shi ko massrauta ta sanar ko ta tuntuɓi gwamnatin jihar Zamfara, ko kuma da hannun Gwamnatin Zamfara wajen bayar da sarautar, sai majiyar ya ce bai sani ba, amma dai, ya tabbata za a yi shagalin naɗin sarautar a ranar Asabar ɗin nan.
Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna Bello Matawalle, Zailani Bappa da Kakakin Yaɗa Labaran Kwamishinan ‘Yan Sandan Zamfara, Mohammed Shehu, ba su amsa kiran da wakilin mu ya yi masu ba. Kuma ba su maida amsar saƙon tes ɗin da ya yi masu ba.
Amma Wakilin Masarautar ‘Yandoton Daji, Magaji Lawali ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa masarautar ta yanke shawarar naɗa wa Aleru Sarkin Fulani a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin ƙarfafa zaman lafiyar da aka samu a yankin.
“Tabbas ina tabbatar maka cewa za a yi bikin naɗin sa. Mu na yin wannan ƙoƙarin ne domin ƙarfafa ɗorewar zaman lafiyar da aka samu. Saboda a da a kullum sai an kashe mutane kuma sai an yi garkuwa da wasu.” Haka ya shaida wa wakilin mu a ranar Juma’a.
A San Mutum A San Asalin Sa: Wane Ne Ada Aleru:
An haifi Ada Aleru a ƙauyen ‘Yankuzo ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Tsare. Amma a cikin gari ya tashi har ya girma.
Aleru ya na da shekaru 45 kuma ya na jagorantar ‘yan bindigar da ke addabar yankin Tsafe, Gusau, Zamfara da Ƙanƙara ta Jihar Katsina.
Yaran Aleru na girmama shi kuma su na jin tsoron sa, saboda irin kisan gillar da ya ke wa waɗanda ya kama.
An zarge shi da kashe ɗan Kwamishinan Tsaro Da Harkokin Cikin Gida na Jihar Zamfara, wato Mamman Tsafe.
Kafin harin da ya kashe ɗan Mamman Tsafe, Aleru ya sha kai hari hare-hare a cikin hedikwatar Ƙaramar Hukumar Tsafe.
Cikin 2019 ne Kwamishinan ‘Yan Sandan Katsina Sanusi Buba, ya ce Rundunar ‘Yan Sanda za ta biya ladar naira miliyan 5 ga duk wanda ya bayar da bayanin inda za a kamo Aleru, kuma har aka kama shi ɗin.
Shi ne ya kai hari a Ƙaramar Hukumar Faskari cikin Jihar Katsina, a Ƙadisau, inda aka kashe mutum 52. Ya kai harin ne saboda nuna fushin ‘yan sanda sun kama ɗan sa mai suna Sulaiman.
Shi ne kuma ake zargin ya kama jami’in Kwastan ɗin da ya ce sai an biya kuɗin fansa naira miliyan 10.
An sha yin zaman sulhu da sasantawa da Aleru a baya. Bayan wani zama da aka yi da shi a cikin Maris, ya ce amma ba zai ƙyale mutanen ƙauyen Magazu da kewaye ba, saboda a cewar sa, su na nuna wa Fulani rashin imani.
Amma dai wani jami’in tsaro da ya nemi a ɓoye sunan sa, ya ce mutanen Magazu da kewaye sun nemi yin zaman sulhu da Aleru kwanaki huɗu da su ka gabata.
An ce an yi zaman sulhu da ɓangaren Aleru da kuma dattawan yankin Magazu.
Mutanen Magazu sun nemi a bar su su yi noma da zirga-zirga. Su kuma ɓangaren Aleru sun nemi mutanen yankin Magazu su daina kashe Fulani.
Yayin da aka yi asarar dubban rayuka a Jihar Zamfara, cikin watan Yuni Gwamna Bello Matawalle ya ce kowa ya yi rajistar mallakar bindiga, domin ya kare kan sa.