Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed, ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta kwashi naira biliyan 1 daga Asusun Rarar Kuɗin Fetur (ECA), domin inganta harkokin tsaro, a daidai lokacin da kuɗaɗen shiga daga fetur ke ƙara raguwa sosai.
Zainab ta yi wannan bayani a gaban manema labarai, ranar Laraba, a fadar Shugaban Ƙasa, ƙarshen zaman su da Shugaba Muhammadu Buhari.
Waɗannan kuɗaɗe da Zainab ta ce an kamfata, lamarin ya zo ne daidai lokacin da ake kukan cewa kuɗaɗen asusun sun ragu sosai da sosai.
Rahotanni sun ce kuɗaɗen da ke cikin asusun sun ragu daga dala miliyan 35.7 a cikin Yuni 2022 zuwa dala 376,65.09 a ranar 25 Ga Yuli, 2022.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa Akanta Janar ne ya bayyana sauran adadin a ranar Talata, amma bai faɗi dalilin raguwar kuɗaɗen ba.
A ranar Laraba dai Minista Zainab ta ce wutsilniyar da kasuwar ɗanyen mai ke yi a duniya ce ta tankwafe asusun har kuɗaɗen su ka ragu.
“Tsawon shekaru huɗu kenan ba mu saka ko sisi a cikin Asusun Rarar Ribar Fetur ba, saboda faɗi-tashin da kasuwar ɗanyen mai ke yi a duniya.” Inji Zainab.
“To abin da mu ke da shi a cikin asusun ne mu ka riƙa cira a hankali ana yin wasu ayyuka da su. Kuma duk lokacin da za a yi amfani da kuɗaɗen, sai an nemi shawarar Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa, wato gwamnoni, saboda asusu ne na Gwamantin Tarayya.
“Kuɗin da aka cira daga asusun a baya-bayan nan, su ne dala biliyan 1 domin a inganta harkokin tsaro. Kuma duk abin da ake cira sai da sanin Gwamnoni.”
Discussion about this post