Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Lawal da tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu dogara, sun ƙara fitowa fili sun nuna rashin amincewar kan takarar Bala Tinubu da Kashin Shettima a APC, takarar da ake kira ‘Muslim-Muslim Ticket’, saboda su biyun duk Musulmai ne.
Babachir Lawal ya ce Kiristoci ‘yan APC za su yi amfani da katin zaɓen su domin su koya wa APC hankali, tunda hankalin ta ya gushe a jikin ta.
Babachir ya ce duk zancen banza ne da ake cewa wai cancanta ce ta sa Tinubu ya ɗauki Kashim Shettima ya yi masa takarar mataimaki, ba addini ba.
Lawal ya ce tsarin ‘Muslim-Muslim’ wata daɗaɗɗiyar ajanda ce ta ture Kiristoci daga mulkin ƙasar nan.
Ya buga misali da ɗaukar Kashim Shettima matsayin mataimakin takarar Tinubu, rashin Kiristoci Kwamitocin NWC da NEC na jam’iyyar APC, ya ce duk tuggun ture Kiristoci ne.
“Kada ma a kawo mana wani rainin wayau a ce wai babu ruwan addini idan ana maganar siyasa. Domin abin da ke faruwa a APC daɗaɗɗen shiri ne sai yanzu aka samu damar fito da shi.
Saboda haka ya ce tun da wuri bai kamata APC ta ci gaba da tafiyar ‘Muslim-Muslim Ticket’ ba, saboda ba wani abin alherin da zai kawo, sai dai ƙara rarrabuwar kawuna tsakanin Musulmi da Kirista a Najeriya.
Shi ma tsohon Kakakin Majalisar Tarayya Yakubu Dogara, ya yi fatali, tir da Allah–wadai da abin da APC ta yi, wanda ya ce babban kuskure ne da rainin wayau a ce duk cikin Kiristocin Arewa babu wanda zai iya zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a APC.
“Tinubu ya yi babban kuskure tunda har ya biye wa gungun waɗanda su ka kitsa tuggun raina mana wayau.”
Dogara ya ce Kiristocin APC za su yi amfani da katin zaɓe domin su koya wa APC hankali.
Cikin manyan baƙi har da Sanata Elisha Agbo da Solomon Dalung.
Discussion about this post