A ranar Juma’a ce Hukumar EFCC ta yi dirar-mikiya a Wuse Zone 4, Abuja, Kasuwar da ‘yan canjin kuɗaɗen waje su ke.
PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa an kai farmaki kamen ‘yan canji ne bayan da hukumar ta gano cewa akwai masu fitar da maƙudan na’urori daga bankuna su na sayen dala su na ɓoyewa.
Majiya a EFCC ta ce dama jami’an hukumar sun kai sati ɗaya su na sa-ido a asirce dangane da yadda ake hada-hadar canjin kuɗaɗe a kasuwar.
Yayin da har yanzu ba a san yawan waɗanda aka kama ba, haka kuma wakilin mu bai san takamaiman kuɗaɗen da EFCC ta kama a Zone 4 ba.
Cikin makon jiya ne dai Babban Bankin Najeriya ya haramta kamfatar kuɗaɗe a sayi kuɗaɗen waje a su, musamman daloli.
Lamari ya ƙara muni yayin da a cikin makon nan dala ta tsula tsadar da har sai da ta kai naira 716.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda dala ta yi wa naira dukan wulaƙancin da sai an biya naira 716 sannan naira za ta yi daidai da dala ɗaya.
A ranar Laraba naira ta yi faɗuwar da ba ta taɓa yin irin ta ba a tarihi, inda sai mutum ya biya naira 716 sannan za a ba shi dala 1.
Sai dai kuma kafin a tashi kasuwar da yamma, naira ta ɗan murmure daga mummunan dukan da ta sha, inda ta koma 670 duk dala 1.
Wannan lamari ne ya sa Sanata Olubunmi Afetumbi daga Jihar Ekiti, ya yi kira a daina sayar da dala ga ‘yan canji, saboda harƙallar da ya ce ana yi.
Ita kuma Sanata Biodun Olujimi, ta ce ya kamata a hukunta waɗanda su ka haddasa karyewar darajar naira.
Majalisar Dattawa a zaman ta na ranar Laraba ta amince a kira Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele domin ya yi bayani.
To sai dai kuma ba a faɗi ranar da zai je majalisa a gana da shi ɗin ba. Ga shi kuma majalissar ta tafi hutu, ba za a koma ba sai ranar 20 Ga Disamba.
A farashin gwamnati kuwa, dai da dala ta kai naira 444 a ranar Talata, amma a kasuwar ‘yan canji ta Uyo, an sayar da dala 1 naira 685.
Tun a farkon watan Yuli ne dai dala ta ƙara kekketa wa naira rigar mutunci daidai lokacin tsadar kayan abinci.
A daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da ƙuncin rayuwa da tsadar kayan masarufi da na abincin da ake nomawa a gida da na waje, darajar Naira na ci gaba da zubewa warwas a gaban Dalar Amurka.
A ranar Talata an wayi gari dala ɗaya ta na daidai da Naira 422.71, a farashin gwamnati, amma kafin yamma sai da ta kai Naira 430. Haka FMDQ ya bayyana a yammacin Talata.
Hakan ya na nufin cewa darajar Naira ta ƙara raguwa da naira 4.25 kenan, idan aka kwatanta da yadda ta ke kan naira 425.75 a kasuwar hada-hadar kafin ranar Talata, wato a ranar Litinin.
Wannan ne zubewar darajar Naira mafi muni a tsawon lokacin da ta sha haɗa ƙwanji da dala.
Tun cikin makonni biyu da su ka gabata ne dala ke nuna wa Naira cewa ‘ruwa ba sa’an kwando ba ne’ a kasuwar hada-hadar tsaye da kuma a farashin gwamnati.
Tsawon makonni biyu an riƙa sayar da dala ɗaya kan Naira 420 zuwa 425 a farashin gwamnati. Amma ranar Talata Naira ta sha dukan tsiya, dala ta yi mata laga-laga, yadda darajar naira ta faɗi ƙasa warwas, zuwa dala ɗaya daidai da Naira 430 a farashin gwamnati.
A kasuwar tsaye ta ‘yan canji a garin Uyo, an riƙa sayen dala ɗaya naira 610, ana sayarwa naira 616 a ranar Talata.
Wani ɗan canji ya bayyana wa wakilin mu cewa dala ta yi ƙaranci, saboda gwamnatin tarayya na ta kulle asusun masu ajiyar dala a bankuna daban-daban.”
Discussion about this post