Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya bayyana cewa muhimmamin dalilin da yasa ya zaɓi Kashim Shettima mataimakin sa shine dattaku da sanin yakamata, da kuma hangen nesa da yake da shi.
Sanata Kashim Shettima ne tsohon gwamnan jihar Barno wanda yanzu haka take wakiltar shiyyar Barno a majalisar Dattawa.
An yi ta ayyana sunaye da dama cewa wai sune Rinubu zai zaɓa mataimakin sa amma kuma sabarwar da yayi a yau bayan ziyara da ya kai fadar shugaban kasa da yammacin Lahadi ya kawo karshen raderadin da ake ta yadawa.
Bayan haka Tinubu ya ce jam’iyyar APC ce za ta yi nasara a zaɓen 2023.
Discussion about this post