A ranar Litinin ne gwamnatin jihar Kano ta sanar da dakatar da masu Keke NAPEP wanda aka fi sani da ‘Adaidata Sahu’ aiki a jihar daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safiya.
Gwamnati ta ce dokar zai fara aiki daga ranar Alhamis 21 ga Yuli 2022.
Kwamishinan yada labarai na jihar Muhammad Garba ya bayyana cewa gwamnatin Abdullahi Ganduje ta yanke wannan shawara ce a zaman da ta yi da jami’an tsaron jihar a fadar gwamnati.
Garba ya ce maķasudin yin haka na da nasaba da matsalolin tsaro a jihar. Yace yin haka zai samar da kariya ga jama’a daga miyagu da ke aikata ta’addanci a jihar.
Ya ce gwamnati ta yi kira ga masu Keke NAPEP da kada su kuskura su rika aiki adaga wannan lokaci wato 10 na dare domin kuwa an saka jami’an tsaro a ko ina sannan da basu dama su kama duk wanda ya karya wannan doka.
Gwamnati ta ce babtun yau ba ta ke samun matsaloli da masu tuka Keke NAPEP a jihar.
Idan ba a manta ba PREMIUMTIMES ta taba buga labarin yajin aikin da ýan Keke suka yi saboda karin haraji da gwamnati ta yi da kirkiro da sabuwar lamba.
Discussion about this post