Tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma tsohon Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa wakilan zaɓen ‘yan takarar da aka ba kuɗi su ka sayar da ƙuri’in su, su ne a sahun gaban matsalolin Najeriya.
Amaechi ya yi wannan zargin yin amfani da kuɗaɗe ne da wani ɗan takara ya yi, ya sa waɗanda su ka fito hannu-baka-hannu-ƙwarya su ka sayar da ‘yancin su don a ba su kuɗin kashe masu talaucin da ke addabar su.
Ya yi wannan zargin lokacin da ya ke jawabi wurin taya murnar cika shekara 60 na Shugabar Cocin Life Evangelic Mission na Fatakwal.
Amaechi wanda ya zo na biyu a zaɓen fidda-gwani da ƙuri’u 316, ya yi na biyu ga Bola Tinubu, wanda ya zo na ɗaya da ƙuri’u 1271, ya ce “Waɗanda ke zaɓen ‘yan takara a wurin fidda gwani da yawanci talakawa ne waɗanda ke fama da talauci ake ɗaukowa daga karkara, a ba su kuɗi su zaɓi wanda ba shi su ka yi niyyar zaɓe ba.”
Ba Amaechi kaɗai ne ya yi zargin an yi amfani da kuɗi wajen zaɓen fidda gwanin APC na ƙasa.
Gwamna Umahi da Tunde Bakare, sun yi takara kuma su ma kamar Amaechi, sun yi ƙorafin wakilan yankunan su sun sayar da ƙuri’un su.
Amaechi ya jaddada cewa waɗannan masu zaɓen su ne matsalar Najeriya.
Shi kuwa Tunde Bakare da bai samu ko ƙuri’a ɗaya ba, cewa ya yi rashin samun ko da ƙuri’a ɗaya ya nuna irin nagartar sa da tabbatar da cewa bai raba ko da Naira dubu ɗaya ba.
An dai zargi Tinubu da amfani da kuɗi ya saye wakilan zaɓen ‘yan takara.
Discussion about this post