A daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da ƙuncin rayuwa da tsadar kayan masarufi da na abincin da ake nomawa a gida da na waje, darajar Naira na ci gaba da zubewa warwas a gaban Dalar Amurka.
A ranar Talata an wayi gari dala ɗaya ta na daidai da Naira 422.71, a farashin gwamnati, amma kafin yamma sai da ta kai Naira 430. Haka FMDQ ya bayyana a yammacin Talata.
Hakan ya na nufin cewa darajar Naira ta ƙara raguwa da naira 4.25 kenan, idan aka kwatanta da yadda ta ke kan naira 425.75 a kasuwar hada-hadar kafin ranar Talata, wato a ranar Litinin.
Wannan ne zubewar darajar Naira mafi muni a tsawon lokacin da ta sha haɗa ƙwanji da dala.
Tun cikin makonni biyu da su ka gabata ne dala ke nuna wa Naira cewa ‘ruwa ba sa’an kwando ba ne’ a kasuwar hada-hadar tsaye da kuma a farashin gwamnati.
Tsawon makonni biyu an riƙa sayar da dala ɗaya kan Naira 420 zuwa 425 a farashin gwamnati. Amma ranar Talata Naira ta sha dukan tsiya, dala ta yi mata laga-laga, yadda darajar naira ta faɗi ƙasa warwas, zuwa dala ɗaya daidai da Naira 430 a farashin gwamnati.
A kasuwar tsaye ta ‘yan canji a garin Uyo, an riƙa sayen dala ɗaya naira 610, ana sayarwa naira 616 a ranar Talata.
Wani ɗan canji ya bayyana wa wakilin mu cewa dala ta yi ƙaranci, saboda gwamnatin tarayya na ta kulle asusun masu ajiyar dala a bankuna daban-daban.”
Discussion about this post