Hedikwatar Hukumar tsaron ƙasa DHQ ta bayyana cewa rundunar ‘Operation Hadin Kai’ sun kashe Boko Haram 42 a Arewa maso Gabashin kasar nan.
DHQ ta ce ‘yan Boko Haram 3,858 ne suka mika wuya ga rundunar ‘Operation Hadin Kai’ inda a cikinsu akwai kwamandoji shida.
Darektan yada labarai na hukumar manjo-janar Bernard Onyeuko ya sanar da haka a Abuja ranar Alhamis yayin da yake bayanin aiyukkan da dakarun sojojin Najeriya ke yi.
Ya ce a ranar 11 ga Yuni rundunar sojin sama dake karkashin ‘Operation Hadin Kai’ sun yi wa Boko Haram ruwan bama-bamai a Tumbum Jaki da Tumbum Murhu dake kusa da tafkin Chadi inda suka kashe Boko Haram sama da 21.
A wannan rana Kwamandoji shida suka mika Kai.
Kwamandojin da suka mika wuya sun hada da Malam Mala Hassan (Wali), Ali Madagali (Munzur), Musa Bashir (Chief Anur), Buba Dahiru (Munzur), Jafar Hamma (Kaid) da Abbali Polisawa.
“Sauran ‘yan Boko Haram din da suka mika wuya sun Kai mutum 3,858 inda a ciki akwai maza 504, mata 1,042 da Yara kanana 2,311. Wadannan mutane sun mika Kai tsakanin ranar 1 zuwa 14 ga Yuli.
Onyeuko ya ce dakarun sun kashe Boko Haram da dama a arangamar da suka yi da su a kauyen Gamage dake karamar hukumar Dikwa sannan da Wanda suka yi da su a hanyar Dikwa zuwa Gamborou zuwa Ngala, da hanyar Pulka zuwa Gwale a jihar Borno.
Ya ce dakarun sun Kuma kama mutanen dake siyar wa Boko Haram kaya inda a cikin su akwai mata biyu masu sunan Hauwa Gambo da Khadija Dirsa.
“A takaice dai dakarun sun kashe Boko Haram 42, sun kama 10,sun kama makamai da suka hada da AK-47 guda 17, bindiga kiran QTC guda daya, RPG daya, bam din hannu 6, harsasai 5mm guda 120 da 7.62mm guda 54 da kuma makamai da harsasai da dama.
Discussion about this post