Ɗan takarar mataimakin shugaban Kasa na jam’iyyar LP Datti Baba Ahmed ya bayyana cewa zaben 2023 ba zaɓen addini ko ƙabilanci bane.
Datti ya faɗi haka a hira da yayi da BBC Hausa inda ya kara da cewa ƴan Najeriya sun dawo daga rakiyar siyasar ƙabilanci ko ɓangaranci.
” Babu waɗanda suke kuka da gwamnati mai ci irin ƴan Arewa wanda suna suka yi ruwa suka yi tsaki dole sai gwamnatin ta yi nasara. Amma kuma ai sune suka fi kowa ɗanɗana kuɗar su. Kuka ake yi ta kowani kusurwa na yankin saboda tsananin da ake dandanawa
” Saboda haka ba wannan karon tasu ta kare. Domin goguwar da zata danno kan APC ta yi wujiwuji da ita sai ya fi irin goguwar 2015. Jam’iyyar LP kamar jirgin kasa ne, amma fa ba irin ta Abuja-Kaduna ba, wannan ba za a iya kada ita da nakiya ba. Kuma duka ƴan Najeriya duk sun ɗare cikinta yanzu.
Babba-Ahmed ya kara da faɗin wasu dalilan da suka sa ya fice daga Jam’iyyar PDP, bayan yayi takarar gwamna a jihar Kaduna.
” Ni ba zan biya daliget don su zaɓe ni ba. Wannan yana saga cikin dalilan da suka sa na fice daga PDP.
” Sannan kuma ay abinda mutane suka manta shine, duk wani ma’aikaci a kasar nan ɗan jam’iyyar LP ne. Saboda haka mune ma muka fi su yawa ba su ba.
Discussion about this post