Makusanci kuma Hadimin babban malamin addinin musulunci dake Kaduna Sheikh Ahmed Gumi, Tukur Mamu ya ce tun kafin ƴan bindiga su kai hari gidan yarin Kuje, ya rika faɗin cewa akwai wannan shiri da suke kullawa amma aka yi masa kunnen uwar shegu.
A wata doguwar takarda da ya aika wa PREMIUM TIMES, Mamu ya ce ya daɗe yana tattaunawa da waɗannan ƴan bindiga, wanda ƴan Boko Haram ne domin ganin an sako fasinjojin jirgin kasan Kaduna-Abuja wanda aka yi garkuwa da su, amma kuma gwamnati bata ɗauki abin da muhimmanci ba.
” Na faɗi wa gwamnati cewa ga bukatun mutanen nan, wanda shine a sakan musu wasu. Kuma har an yi nisa a tattaunawar da ake yi amma da ya ke ba rayukan talakawa bane a gaban gwamnati ta yi watsi da wannan tattaunawa.
” An samu a sako wasu daga cikin fasinjojin su 10 bayan amincewa da aka a tsakanin ƴan bindigan amma kuma sauran alkawarin da aka ɗauka sai gwamnati ta watsi da su. Daga nan ƴan bindigan suka aika sakon cewa daga wannan mako za su fara yanka sauran mutum 51 dake tsare a wurin su.
Mamu ya ce gwamnati ba ta ce komai a kai ba. ” Abun mamaki shine yadda gwamnati ke yi kamar ba rayukan mutane take wasa da su ba.
” Ni fa nawa taimako ne in ga yadda Allah zai sa a iya ceto mutanen nan dake tsare hannun ƴan bindigan amma duk kokarin da na yi ko nake yi a banza. Tun da gashi maimakon a bi tsarin da aka faro tun farko domin a saki sauran mutum 51 dake tsare hannun ƴan bindigan, sannan a samu matsaya game da bukatun su, sun zo sun fasa inda mutanen na su ke tsare sun kwashe illahirin su kaf har da waɗanda ba su cikin su sun arce saboda halin ko in kula na gwamnati.
” Da an bi shawara ta da tun farko hakan bai faru ba. Saboda haka ni daga yanzu na hakura da cigaba da tattauna da ƴan bindigan. Na zame hannu na na kyale gwamnati ta yi abinda ta ga dama. Tunda gara ace wasu kalilan na handame dukiyar talakawa maimakon a ce an yi abinda ya dace an ceto rayukan waɗanda basu ji ba basu gani ba
Discussion about this post