Gogarman ɗan ta’adda da ka naɗa sarkin Fulani Yandoto Aleru Ada ya yi kurin cewa shi baya sace mutane idan ya kai farmaki garuruwa.
” Na fi ƙarfin sace mutane, kashe su na ke yi. Amma yara na na yin haka.”
A tura tattauna wa da da Aleeu yayi da BBC ya bayyana cewa dalilin da ya sa ya ke kashe mutane kuwa shine ” Yadda ake muzguna wa Fulani makiyaya. An muzguna musu, anyi watsi da su kamar ba ƴan kasa ba. Sojojin sama na kashe su sannan duk inda suke bi su yi kiwo duk an kwace, babu su yanzu. Waɗannan su ne dalilan da ya sa ninma.ba zan bar mutane su huta ba.
Shi ko ɗan ta’addan da ya jagoranci sace yaran makarantar mata na Jangebe ya bayyana cewa sai da ak biya su naira miliyan 60 kafin suka sako ɗaliban.
” Sai da aka biya naira miliyan 60 kafin muka sako ɗaliban makarantan da muka sace, kuma majamai mula siya da kuɗin.
Ƴan ta’adda na gallaza wa mutane a yankin Arewa Maso Yamma. Iyaye sun ga yadda ake kashe musu ƴaƴan su a gaban su, a yanka su kamar dabbobi. Da yawa sun easa matsugunan su sannan wasu sun rasa na kusa da su a dalilin ta’addancin da ya ki ci yaƙi cinyewa.
BIDIRI DA DIDIMA KAN ƘABURBURAN ZAMFARAWA: Yadda aka sha shagalin naɗin gogarma Aleru da sanin Gwamnatin Zamfara
A ranar Asabar ce Sarkin ‘Yandoton Daji, Aliyu Marafa ya naɗa Adamu Aleru da aka fi sani da Ada Aleru sarautar Sarkin Fulanin ‘Yandoton Daji.
Sai dai kuma kwana ɗaya bayan naɗin, Gwamnatin Jihar Zamfara ta bada sanarwar soke naɗin tare da kafa kwamitin binciken yadda aka naɗa shi. Sannan kuma an dakatar da Sarkin ‘Yandoton Daji Aliyu Marafa.
Sai dai kuma PREMIUM TIMES Hausa ta tabbatar da cewa gwamnatin Zamfara na da masaniyar za’a yi naɗin, tun ma kafin ta buga labarin cewa za a yi naɗin a ranar Asabar.
Tataɓurza A Ranar Naɗin Aleru:
Wannan jarida ta gano cewa an yi ƙoƙarin hana naɗin a ranar Asabar, inda aka riƙa taro nan da can domin a hana taron naɗin.
Sai dai kuma kafin lokacin tuni Aleru ya gama shiri, kuma yaran sa sun cika gari. An yi taro a Ƙaramar Hukumar Tsafe, inda da farko aka nemi a hana taron, amma kuma aka nuna wa gwamnati cewa Aleru fa ya fusata jin cewa ba za a naɗa shi ba.
Majiyar mu ta ce Aleru tuni ya sa an yanka shanu 17 da raguna masu yawan gaske, domin ya ƙasaitaccen biki bayan naɗin sa, a ƙauyen Munhaye.
Majiya ta ce an sanar da gwamnatin Zamfara cewa ya zama wajibi a ci gaba da yin bikin naɗin, domin idan aka fasa, “Aleru zai iya huce haushin sa a kan mutanen yankin, ta hanyar sake kai masu sabbin hare-hare.
An dai tsara za a naɗa Aleru ƙarfe 11 na safe, amma ba a yi ba sai ƙarfe 2:45 na Yamma.
Bayan an naɗa shi, Aleru ya ce zai yi bakin ƙoƙarin sa ya ga an daina kai hare-hare a yankin.
Ya yi zargin cewa akwai wasu manya masu amfana da hare-haren Zamfara su na kuɗancewa, amma dai bai ambaci sunayen su ba.
Sannan kuma ya ce shi da yaran sa ba ‘yan bindiga ba ne, masu neman ‘yanci ne da kuma kare kan su.
Manyan jami’an Gwamantin Zamfara da su ka halarci taron naɗin, sun haɗa da Kwamishinan Harkokin Tsaro da Cikin Gida na Zamfara, Mamman Tsafe, Mashawarci Kan Harkokin Tsaro na Zamfara, Abubakar Dauran Shugaban Ƙaramar Hukumar Tsafe, Aminu Mudi, jami’an gwamnati da Dagatai da sauran su.
Hakan ya nuna cewa da sanin Gwamnatin Zamfara aka yi taron, domin hatta Kwamishinan Yaɗa Labarai ma ya tura wakilci.
Kakakin Fadar ‘Yandoton Daji Bello Yusif ya shaida wa wakilin mu cewa da sanin Gwamnatin Zamfara aka yi naɗin, domin babu yadda za’a yi ba tare da an sanar da gwamnati ba.
Da yawan ‘yan bindiga irin su Isuhu, Ɗanbokolo, Turji, Ali Zakwai, Sanata da Maishamuwa sun yi niyyar zuwa, wasu ma su na can wajen gari a cikin daji sun yi sansani a daji, amma da yaran su na cikin gari su ka sanar da su an ɗage naɗin, sai su ka juya su ka koma abin su.
Shi kan sa Aleru bai je wurin naɗin ba sai da La’asar.
Wani masanin sarautar gargajiya mai suna Yahuza Getso, ya shaida wa wakilin mu cewa naɗin Aleru Sarkin Fulani ya tabbatar da abu biyu. Na farko dai martabar sarautar gargajiya ta zube. Na biyu kuma gwamnati ta san ‘ysn bindiga da kuma duk inda su ke.
Discussion about this post