Buhari ya taya Adeleke murnar lashe zaɓen Osun, ya ce mutanen Osun sun zaɓi abinda suke so ne.
Idan ba a manta ba, an gudanar da zaɓen gwamna na jihar Osun a ƙarshen wannan mako inda jam’iyyar APC ta sha kayi a hannun PDP.
Wannan kayi na da nasaba da hamayyar da wasu ke ganin mutanen jihar ke yi da jagoran siyasar Yarabawa, Bola Tinubu, inda suke ganin ya yi musu karfa-karfa ne wajen tilasta gwamna maici ya cigaba da mulki.
Mutanen garin sun fito manyan tituna inda suka rika yin biki da nuna jin dadin su kan abin da ya auku.
Shugaba Buhari ya bayyana a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya ce jama’ar Jihar Osun sun zaɓi ra’ayinsu ta hanyar jefa ƙuri’a a inda suke so. Kuma ya kara da cewa dole a girmama zaɓen mutune.
Buhari ya bayyana cewa gudanar da zaɓen da aka yi lafiya wata alama ce da ke nuna cewa an samu ci gaba da kuma haɗin kan masu ruwa da tsaki da kuma hukumar zaɓe da jami’an tsaro da jam’iyyu da yan jarida da ƙungiyoyi masu zaman kansu da masu zaɓe domin ƙara inganta harkar zabe a Najeriya.
A karshe ya kuma jaddada aniyarsa ta gudanar da ingantaccen kuma sahihiyar zaɓe a lokacin mulkinsa.
Wannan rashin nasara ya yi matukar tada wa APC hankali domin daga wannan zaɓe sai zaɓen gamagari wanda za ayi a watan Faburairun 2023, kuma ga dukkan alamu ga ƴan Najeriya idan ta ruwa rijiya, idan bata yi ba masai.
Discussion about this post