Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya jaddada matsayarsa game da yadda ya kamata a tunkari matsalar ta’addanci a kasar nan
A hira da yayi da gidajen radiyo a Kaduna ranar Laraba, El-Rufai ya ce har yanzu na nan a kan bakan sa cewa abi ƴan ta’adda inda suke a darkakesu.
” Ina nan akan baka ta cewa abi ƴan ta’adda can cikin ƙurgurmin daji a gama da su ta sama da ta kasa, ba wai a riƙa jira sai sun kawo hari sannan jami’an tsaro su far musu.
El-Rufai ya kara da cewa idan ma waɗanda ke Abuja basu yarda da irin lalacewa da kuma kara karfi da ƴan ta’adda suke yi bane, yanzu ta zo gida, kusa da su a Abuja
” Da ma Zamfara, Kaduna, Sokoto da Neja ne abin yayi muni, toh yanzu sun dira har Kuje kowa ya gani. Kila waɗanda abin ke hannun su a Abuja za su maida hankali yanzu.
” Na nemi in ga Buhari bayan sakin bidiyon da ƴan ta’adda suka ce za su sace shi da ni. Da na gan shi ina yi masa bayani a kai, ashe bai san da wannan bidiyo ba sai da na zo na gaya masa. Gwamnan Zamfara Matawalle ya daɗa tabbatar masa cewa shi ma ya ga bidiyon.
” Tsakani da Allah a ce wai ya kai ga ƴan ta’adda suna fitowa kirikiri suna cewa sai sun sace shugaban kasa sukutum din sa, da me yayi kama. Dole a maida hankali matuka a kawo karshen wannan abu cikin gaggawa.