Wata rana a safe cikin watan Afrilu, wasu ƙananan yara mata na gudun rige-rigen isa rijiyar burtsatse domin su ɗebi ruwa, sun riƙa gudu su na wasan kokawa da juna a cikin raha da annashuwa, duk kuwa da cewa a ƙauyen na su Kurebe, da ke cikin Ƙaramar Hukumar Shiroro a Jihar Neja, ‘yan Boko Haram sun hana su sakat.
Ai Maryam Lawal, Hafeezah Bashir, Shamsiyyah Lawal, Shafa’atu Jamilu, Asma’u Isa da Hakuni Ɗanlami na tsakiyar wasan turerwniya a jikin burtsatse, sai jirgin yaƙin Sojojin Saman Najeriya ya wuce ta saman su, ya sako bam, ji ka ke daram!
Hayaƙi da ƙura su ka murtuke ƙauyen, wasu gidaje su ka lalace, bishiyoyi da dama su ka karairaye. Bayan ƙura ta lafa, mutane su ka zabura wurin da yaran nan ke wasa. Sai aka tarar da naman jikin su ya dagargaje, babu wadda za a iya tantancewa a wannan wance ce.
Sojojin sama sun kai harin ne bisa wani rahoton sirri da aka ba su, amma na ƙarya. An ce masu dukkan mutanen da ke cikin ƙauyen Kurebe sun gudu, sai ‘yan Boko Haram ne kaɗai a cikin ƙauyen.
PREMIUM TIMES ta tattauna da mutanen gari, manoma da ‘yan tiredar garin da kuma iyayen waɗanda aka kashe wa yara. An yi tataunawar bayan gwamnatin jihar Neja da hukumomin sojoji sun ƙaryata kashe fararen hula a Kurebe.
Lamarin ya yi wa jama’ar Kurebe muni, domin an jefa masu bam daidai lokacin da ‘yan Boko Haram ke kashe su, yi wa wasu fyaɗe da kuma kama yaran su matasa su na tilasta su ɗaukar makamai su shiga ta’addanci.
“Bam ya yi kaca-kaca da naman jikin su, har ba a iya tantance wannan wance ce ko wance ce. Sai aka yi masu ƙaburbura uku, aka riƙa tattara naman jikin su ana rufewa.” Inji Musa Dobi, wanda aka kashe wa ‘yar uwar sa.
Yadda Mu Ke Tsoron ‘Yan Ta’adda, Haka Mu Ke Tsoron Sojoji -Dobi
Dobi ya riƙa magana ya na kuka da murmushi a lokaci guda. Da wakilin mu ya tambaye shi dalilin yin haka, sai ya ce “ai kukan na bakin ciki ne. Murmushin kuma na mamakin yadda gwamnati ta ce ƙarya mu ke yi wai ba a jefa bam har ya kashe yaran mu.
“To a yanzu ba mu sani ba, sojoji za mu fi jin tsaro ko kuwa ‘yan ta’adda?”
A ranar 21 Ga Afrilu, Salis Sabo na Kungiyar Ci Gaban Shiroro ya fitar da labarin wannan bam da ya yi masu ɓarna, wanda ya ce an jefa bam ɗin a ranar 13 Ga Afrilu.
Washegari ranar 22 Ga Afrilu, Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Ahmed Matane ya ƙaryata labarin sojojin sama sun kai hari sun jefa wa talakawan Kurebe bam. Matane ya ce, “labarin na bogi ne, ba gaskiya ba ne.”
Kalaman Matane sun fusata matasan Kurebe da Shiroro, har su Sabo su ka je Minna su ka shaida wa ‘yan jarida cewa za su kai iyayen yaran da aka jefa wa bam, domin a yi intabiyu da su kowa ya ji gaskiyar lamarin.
Sai dai kuma Gwamnatin Jihar Neja ta gaggauta umartar basaraken Kurebe cewa kada ya bar mutanen su je Minna don su gana da manema labarai.
Sojojin Saman Najeriya Sun Ƙaryata Jefa Bam A Kurebe:
Kakakin Yaɗa Labaran Rundunar Sojojin Sama ya shaida wa wakilin mu cewa, “ka je ka yi amfani da abin da Gwamnatin Jihar Neja ta faɗa. Ka daina ‘yan sinsine-sinsinen neman abin da babu.”
PREMIUM TIMES ta samu tattaunawa da dukkan iyayen waɗanda aka kashe ɗin, wanda su ka yi mamaki a cikin damuwa kan yadda gwamnati da sojojin saman Najeriya su ka murje idanun su ka ce ba a kashe kowa ba.
Isa Zariah na cikin waɗanda aka tattauna da su. An kashe masa ‘ya’ya biyu, Asma’u da Shamsiyyah. Kuma an kashe masa jikoki biyu, Maryam da Hafeezah.
Wannan jarida ta kuma tattauna da Bashir Lawal, surikin Isa Zariah, wato mahaifin Maryam da Hafeezah kenan.
Kame-kamen Gwamnatin Neja:
Bayan bayanan Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Ahmed Matane ya ƙaryata labarin aka kai farmakin, shi ma Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Neja, Emmanual Umar, ya jajirce cewa lokacin da Sojojin Sama su ka kai hari a ƙauyen Kurebe, babu farar hula a cikin garin ko ɗaya, sai ‘yan Boko Haram.
Sai dai kuma binciken da PREMIUM TIMES ta yi ƙwaƙƙwaran binciken cewa ƙarya ce kawai da rufa-rufa gwamnati ke yi.
Discussion about this post