Mambobin Majalisar Tarayya ‘yan PDP sun bi yayyen su Sanatocin PDP, inda su ma su ka bai wa Shugaba Muhammadu Buhari wa’adin makonni shida ya shawo kan matsalar tsaro, ko kuma su fara shirye-shiryen tsige shi.
Mambobin sun yi ganawa ce ranar Alhamis a Majalisa, ƙarƙashin jagorancin Sanata Phillip Aduda, ɗan PDP da ke wakiltar Gundumar FCT Abuja a Majalisar Dattawa.
Bayan tashi daga taron, Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Tarayya, Ndudi Elumelu, ya shaida wa manema labarai cewa su ma sun bayar da wa’adin makonni shida ga Shugaba Buhari ya shawo kan matsalar tsaro. Idan aka sati shida babu wani ci gaba, to za su fara shirye-shiryen tsige shi.
A ranar Laraba ce Elumelu ya shawarci ‘Yan Majalisar Tarayya ya ce duk su fece zuwa gida, Abuja ba tsaro.
Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Tarayya, Ndudi Elumelu, ya yi kakkausar shawara ga dukkannin ‘Yan Majalisar Tarayya cewa duk wanda ya tafi hutun da ai fara daga ranar Laraba, to ya ƙaurace wa Babban Birnin Tarayya Abuja, tunda dai birnin ya na fama da matsalar tsaro.
Elumelu ya yi wannan jan hankalin ne a ranar Laraba, lokacin da aka rufe zaman majalisa, aka tafi hutun watanni biyu.
Majalisar Tarayya ta fara hutun wanda sai ranar 20 Ga Satumba za a koma bakin aiki.
“Ina ba ‘yan uwa na ‘yan majalisa shawara, duk wanda ya tafi hutu, to ya fita daga Abuja. Ya je Mazaɓar sa ya zauna tunda dai birnin na fuskantar barazanar tsaro.” Inji Elumelu.
Sai dai kuma Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya ya ja kunnen sa cewa bai kamata ya siyasantar da matsalar tsaro ba.
Furucin na Elumelu ya zo ne kwanaki biyar bayan ‘yan ta’adda sun yi barazanar sace Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Nasiru El-Rufai na Kaduna.
Sannan kuma ranar Juma’a da dare ‘yan ta’adda su ka kai wa dogaran tsaron Buhari hari, su ka kashe sojoji takwas.
Mahara sun kai wa Dakarun sojojin Bataliya ta 7 ta Dogaran Shugaban Ƙasa hari.
Farmakin ya faru a ranar Juma’a da dare, a yankin Bwari da ke Abuja, har su ka kashe sojoji uku, su ka ji wa takwas rauni.
Biyu daga cikin sojojin da aka kashe ɗin manyan jami’ai ne, Kaftin da Laftanar sauran kuma sojoji ne.
Majiya ta ce niyyar ‘yan ta’addar ita ce su je su yi garkuwa da ɗaliban Makarantar Koyon Aikin Shari’a da ke Bwari. Ana jin ma maharan sun yi sansani ne a dajin yankin Bwari.
Hukumar Sojojin Najeriya ba su ce komai ba kan harin. Shi ma Kakakin Sojoji Onyema Nwachuku bai ɗauki kiran wayar da wakilin mu ya yi masa ba.
Amma majiyar leƙen asiri ta sirri daban-daban sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa gwamnati na sane da za a kai farmakin, domin an ƙara matakan tsaro a birnin.
A ranar Litinin an rufe Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Yankin Kwali kusa da Abuja, bayan da ‘yan ta’adda su ka kai hari cikin wata unguwa kusa da makarantar.
Harin da aka yi wanda aka kai wa Dakarun Shugaban Ƙasa, waɗanda aikin su shi ne kare lafiyar shugaban ƙasa, ya faru bayan makonni biyu da kai wa tawagar rakiyar shugaban ƙasa a Dutsinma, Jihar Katsina.
A ranar ce kuma aka kai wa Kurkukun Kuje hari a Abuja, inda su ka kuɓutar da dakarun su na ta’addanci, da sauran ɗaruruwan ɗaurarru.
Harin ranar Juma’a ya zo kwanaki biyu kafin ‘yan ta’addar jirgin ƙasa su ka nuno bidiyon da su ke dukan fasinjojin da su ka tsare a hanyar Abuja-Kaduna.
Cikin bidiyon har barazana su ka yi cewa za su kamo Shugaba Buhari da Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna.
Tabbas An Kai Wa Dogaran Shugaban Ƙasa Hari -Yahaya Bello:
Gwamna Yahaya Bello ya tabbatar da harin da aka kai wa Dakarun Shugaban Ƙasa a Bwari.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna Bello, mai suna Mohammed Onogu ya fitar, ya ce Gwamna ya yi ta’aziyyar waɗanda su ka rasa rayukan su, kuma ya yi jimamin waɗanda aka ji wa ciwo.
Yahaya Bello ya tabbatar da cewa manyan jami’an sojoji biyun da aka kashe, ‘yan jihar Kogi ne.
Ya bayyana kisan su da cewa rashin imani ne, kuma ya yi ta’aziyya ga iyalan su da su ka haɗa da mahaifin Laftanar Suleiman, Kanar Suleiman Ahmodu Babanawa Mai Ritaya da Kaftin Samuel Atta daga Ibaji.
Bello ya yi wa Rundunar Sojojin Najeriya ta’aziyya da jaje.
Discussion about this post