Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa rainin hankali ne kawai barazanar da sanatocin jam’iyyun adawa su ka yi, yayin da su ka yi barazanar sai an tsige Shugaba Muhammadu Buhari.
Sanatocin sun nemi a tsige Buhari ne idan ba zai iya magance matsalar tsaro da ta dabaibaye ƙasar baki ɗaya ba.
Sanatoci daga jam’iyyun adawa sun fice daga zauren Majalisar Dattawa a ranar Laraba, bayan da Shugaban Majalisa ya ƙi bayar da lokaci a karanta roƙon tilasta wa Buhari magance matsalar tsaro a cikin makonni shida, ko kuma a tsige shi kawai.
Bayan ficewar su, hasalallun sanatocin sun shaida wa manema labarai cewa ai da farko sun amince su da sanatocin APC a wani taron sirri cewa a bai wa Shugaban Ƙasa makonni shida.
A raddin da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar, Garba Shehu, Kakakin Yaɗa Labaran Buhari ya bayyana barazanar da sanatocin su ka yi cewa yarinta ce kawai ke ɗibar su. Ya ce batun tsigewa kuma rainin hankali ne.
“Irin wasan yaran da sanatocin su ka yi, su ka fice daga Majalisar Dattawa abin rainin hankali ne. Hana a saurare su da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya yi kuma daidai ne.” Inji Garba Shehu.
“Maimakon su riƙa raina wa masu jefa ƙuri’a hankali, ta hanyar kwaikwayon abin da su ke gani ana yi a siyasar Amurka, ya kamata masu adawa su taimaka a magance matsalolin da Najeriya ke fuskanta, irin su halin ƙuncin rayuwa da aka shiga duk duniya.
Shehu ya ce, kalaman su kawai neman suna ne su ke so don a buga su a shafukan jarida, amma ba kishin ƙasa ba.
Ya ce Gwamnatin Buhari na ƙoƙarin ta wajen ganin ta shawo kan matsalolin ƙasar nan, har da waɗanda ta gada daga gwamnatin PDP a Kudu maso Kudu, Arewa maso Gabas da sauran yankunan faɗin ƙasar nan.
Ya ce ko kwanan nan an ƙara ceto ‘yan matan Chibok.
Shi kuwa Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed, ya bayyana cewa ba sai an bai wa Shugaban Ƙasa wani wa’adi ba, domin ya na bakin ƙoƙarin sa, kuma zai ruɓanya ƙoƙarin da ya ke yi.
Ya jinjina wa sanatocin da su ka nuna damuwar su, inda ya ce sun nuna su na kishin ƙasar su.
Discussion about this post