Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata labarin da wata jarida ta buga, inda ta ce Hukumar Tsaro ta SSS ta aika wa Shugaba Muhammadu Buhari rahoton shawarwari dangane da batun ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Bola Tinubu a jam’iyyar APC.
Garba Shehu, Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Buhari ne ya fitar da sanarwar a ranar Juma’a, inda ya shawarci ‘yan Najeriya cewa su yi watsi da labarin, duk ƙarya ce tsagwaron ta kawai.
Duk da cewa Garba Shehu bai ambaci sunan jaridar ba, amma dai a ranar Laraba jaridar Peoples Gazette ta wallafa cewa wai Hukumar SSS ta yi gargaɗin cewa “takarar Musulmi shugaba kuma Musulmi mataimakin sa, za ta iya hargitsa Najeriya.”
Jaridar ta ce ta samu bayanin ce ƙunshe a cikin wasu bayanan sirri da aka gulmata mata, sai kuma hirarrakin da ta ce ta yi da wasu jami’an leƙen asiri.
A raddin da mayar, Garba Shehu ya shawarci “duk wani wanda ya san ya kamata mai hankali, ya yi watsi da labarin, abin dariya ne kawai wata jaridar yanar zigo ta rubuta wa jama’a shifcin-gizo, domin kawai ta haddada rabuwar kawuna, kuma ta kawo ruɗani a kan zaɓen da ɗan takarar APC a zaɓen Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu ya yi wa tsohon Gwamna Kashin Shettima matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.”
Idan ba a manta ba, bayan Tinubu ya bayyana Kashim Shettima a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, ya ce ya ɗauke shi ne ba saboda addinin su ɗaya ba, sai don cancantar sa kawai.
Tinubu ya ce duk da ya san akwai damuwa daga wani ɓangare, saboda zaɓen mataimakin sa Musulmi, tunda shi ma Musulmi ne, amma dai bai yarda cewa batun addini ne zai zama abu mafi cancanta wajen zaɓen ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa ba.
Discussion about this post