Shugaban Jami’ar Maryam Abacha da ke Maraɗi da Kano Najeriya, Farfesa Adamu Gwarzo ya bayyana cewa babban burin sa a rayuwa kafin ya koma ga mahalicci shine ya ga miliyoyin yara sun samu ilimi.
Farfesa Gwarzo ya kara da cewa buri da yake da shi na ganin yara sun samu ilimi ya sa gaba ɗaya rayuwarsa ta ta’allaƙa a harkar samarwa da inganta fannin ilimi a ƙasar nan.
” Akwai sama da ɗalibai dubu da ke karkashin tallafin karatu nawa wanda nine nake daukar nauyin su. Sannan kuma ba wai na tsaya haka bane ina cigaba da haka.
Game da yajin aikin da jami’o’in gwamnati ke yi a kasar nan, farfesa Gwarzo ya ce wannan matsalace wanda ya kamata a maida hankali akai matuka sannan masu ruwa da tsaki su bada gudunmawa domin ganin an kawo karshen sa.
” Jami’o’i masu zaman kansu ba za su iya ɗaukar yawa-yawan yara da ke tasowa a kasar nan ba. Dole sai na gwamnati ne zata iya ɗaukar mafi yawa daga cikin yaran saboda karfin arziki na iyaye. Wasu dole sai na gwamnati ne za su iya kai yaran su.
” Saboda haka ba ni cikin irin waɗanda ke ganin jami’o’i masu zaman kansu su yawaita don a karya na gwamnati.
Dangantakar Jami’ar da Maryam Abacha
Farfesa Gwarzo ya ce babu wani abu da ya haɗa jami’ar Maryam Abacha da uwargidan marigayi Sani Abacha.
” Na saka sunan Maryam Abacha ne saboda darajata domin uwa ce a wurina. Amma babu wani abu na kuɗi da ya haɗa ta da mu.
Farfesa Gwarzo sananne ne wajen harkar samar da ilimi a nahiyar Afrika.
Shine shugaba kungiyar manyan jami’o’i masu zaman kansu na nahiyar Afrika.
Discussion about this post