Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin sa ba za ta biye wa farfagandan ‘yan ta’adda ba domin kuwa jami’an tsaro na iya kokarin su don ganin sun ceto fasinjojin jirgin kasa da aka sace da kuma gamawa da ‘yan ta’adda.
A sanarwar da Garba Shehu ya fiddda ranar Lahadi, bayan bidiyon da ‘yan ta’adda suka fitar ya karade shafukan yanar gizo da ke nuna suna jibgar fasinjojin Buhari ya ce nan ba da dadewa ba dakarun Najeriya za su gama da ‘yan ta’addan.
” Ba za mu fito kafafen yada labarai muna fadin tsarin da muke yi ba, amma ina so in tabbatar muku cewa dakarun Najeriya a shirye suke kuma suna bibiyar dukkan abinda ke faruwa kuma za su ceto fasinjojin da suka rage ba tare da an rasa wani ko wani ya ji rauni ba.
” Ina so jama’a su sani cewa shugaba Muhammadu Buhari ya yi iya abain zai iaya yi a matsayin sa na shugaban kasa domin kawo karshen ta’addan ci a kasar nan ta hanyar kara wa rundunar tsaron kasa karfin makamai da sauran duk abinda suke bukata. Saboda haka cika aiki kawai nake jira in gani daga dakarun Najeriya.”
Sai dai kuma mutanen Najeriya sun gaji da jin irin haka da fadar shugaban kasa inda a kullum abu mai kaman yaka ya auku sai shugaba buhari ya fito ya rika cewa nan bada dadewa ba za a gama da su.
Discussion about this post