• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Ni da kai na zan zaɓi wanda zai gaje ni, goyon bayan ku kawai nake bukata – Buhari ga Gwamnoni

    Duk da ƙalubalen da mu ke fuskanta, Najeriya za ta ci gaba da zama ƙasa ɗaya dunƙulalliya – Buhari

    MATA KU RIKA SAKA JIGIDA: Sirrika 6 da saka jigida ke yi wa mace – Binciken Masana

    Yadda sojojin sama sun ragargaza sansanonin ‘yan bindiga a jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto da Kaduna

    Yadda rundunar sojin sama suka kashe fitaccen dan bindiga, matan sa biyu da kwamandojinsa 8 a Katsina

    A shafe tarihin wadanda suka soke koyar da tarihi a makarantun Najeriya – Wole Soyinka

    Wole Soyinka ya yi tir da bidiyon barkwanci da shegantakar ‘yan ƙungiyar ‘Pyrates Confraternity’ kan Tinubu

    Duk masu son shugabancin Najeriya su fito su nuna fuskokin su, ba sai lokaci yayi a hadamu da tarkace ba – Muhammadu Sanusi II

    Cire ni daga Sarautar Kano ba zai hana ni ci gaba da faɗin gaskiya ba – Sanusi Lamiɗo

    NDLEA

    Jami’an NDLEA sun kama Faston Coci da durum uku cike makil da muggan kwayoyi

    ‘Yan sanda sun damke faston da ake zargin yayi wa ‘yar shekara 19 fyade

    Ƴan sanda sun kama mutumin da ya saba Yi wa mata fashi bayan ya zuba musu maganin barci a lemu

    Na zaɓi wanda zai yi mini mataimaki, sunan sa na nan a ƴar takarda a gaban aljihuna na cakale – Tinubu

    Lauya ya maka INEC kotu, saboda zargin akwai dungu cikin fam ɗin takarar da Tinubu ya cike

    Ana batakashi tsakanin ‘yan ta’adda da Sojojin Najeriya a Madallah Abuja

    Najeriya ta tsaurara tsaron kurkukun Katsina, Kebbi da Gusau, don hana farmakin ‘yan ta’adda

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    LMC ta ci tarar Kano Pillars, ta kori shugabanta, Jambul bayan ya gobza wa ‘Rafiri’ naushi a haɓa

    Inganta Rayuwar Matasa Ta Hanyar Wasan Kwallon Kafa Da Gudunmawar Al’Ummah A Jigawa, Ahmed Ilallah

    CHAMPIONS LEAGUE: Ko dai tsinuwar Yaya Toure ta yi tasiri kan Pep Guardiola?

    PILLARS SUN KIRA RUWA: Daga yanzu a Abuja za su rika wasan gida kuma an zaftare musu maki 3

    Yadda Kanawa suka yi ragaraga da motar ƴan  Katsina United saboda Pillars ta buga kunnen doki a Kano

    GHANA vs NAJERIYA: Ko Najeriya za ta kauce wa ɗauko buhun kunya na 26 a hannun ‘Black Stars’?

    Barcelona ta yi wa Madrid dukan kabarin kishiya, ba sani ba sabo ta zura mata kwallaye 4 babu ko ɗaya

    ‘CHAMPIONS LEAGUE’: Yadda Benzama ya ceto Madrid daga rijiya gaba dubu, ya kori PSG kuma ya dawo da martabar sa a duniyar ƙwallo

    YAƘIN UKRANIYA YA CI ƘUNGIYAR CHELSEA: ‘Zan sayar da kulob ɗin na sadaukar da kuɗin ga tallafin waɗanda yaƙin Ukraniya ya kassara’ -Abramovich, mai ƙungiyar kuma ɗan asalin Rasha

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

    2023: Ɗan takarar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ziyarci masarautar Dutse

    LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda ƴaƴan jam’iyyar APC da dubban mutanen Kaduna suka yi wa Sanata Uba Sani goma ta arziki

    BIDIYO: Shin zaka iya zama da mai dauke da cutar Kanjamau? – Ra’ayoyin mutane

    Dalilin da ya sa muka yi tattaki har Dubai domin taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar ta – Matan Gwamnonin Najeriya

No Result
View All Result

Ba mu da masaniyar ɗaukar tsohon ɗan Boko Haram aikin tsaron gidan kurkuku -Babban Kwanturolan Kurkuku

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
July 14, 2022
in Labarai
0
KWANAKI 100 BAYAN HARIN JIRGIN ƘASAN ABUJA: Yadda Boko Haram su ka ruguza Kurkukun Abuja, su ka ƙwaci dakarun su 64 da ke tsare

Shugaban Hukumar Kula da Gidajen Kurkuku na Ƙasa, Haliru Nababa, ya bayyana cewa ba shi da masaniyar an ɗauki tsohon ɗan Boko Haram aikin tsaron gidajen kurkuku.

Tsohon ɗan Boko Haram ɗin da ake magana dai shi ne Wilberforce Yohanna, wanda Premium Times ce ta buga labarin ɗaukar na sa a labaran jaridar na makon jiya.

Nababa ya yi wannan iƙirarin na rashin sanin ɗaukar Yohanna, a lokacin da ake tattaunawa da shi a shafin Tiwitar, wanda PREMIUM TIMES ce ta shirya tattaunawar.

An yi tattaunawar ce kan makomar biyo bayan Boko Haram ɓangaren ISWAP sun kai wa Kurkukun Abuja da ke Kuje.

Kwanturolan Kurkuku ya ce ba a sanar da shi cewa Yohanna, wanda ke da lambar ɗauka aiki ta ‘Mataimakin Jam’i (Assistant Cadre) ASC11 da ke aiki Gidan Kurkukun Yola cewa tsohon ɗan Boko Haram ba ne, har sai da ya karanta binciken da PREMIUM TIMES ta buga.

Sai dai kuma ya ce Hukumar Kula da Gidajen Kurkuku ta Ƙasa ta kafa kwamitin binciken lamarin.

“Wato gaskiyar magana ba a kawo min wani abu mai kama da ɗaukar tsohon ɗan Boko Haram ba.” Inji shi.

Duk da Haliru ya ce ba a sanar da shi ba, amma kuma PREMIUM TIMES ya samu kwafen wata takardar gargaɗi wadda ta riƙa yawo a cikin hukumar mai ɗauke da cewa an fa gano Yohanna tsohon ɗan Boko Haram ne.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga Rahoton Musamman, kan yadda aka bankaɗo tsohon ɗan Boko Haram ya zama Jami’in Gidan Kurkuku, watanni biyar kafin farmakin Kurkukun Kuje. Amma kuma mahukuntan hukumar su ka binne maganar, har sai da wannan jarida ta fallasa, sannan maganar ta fito fili.

Ga Labarin Nan:

Mai barci ya tashi, na tsaye ya zauna, mai tafiya ya dakata ya sha labarin yadda tsohon ɗan Boko Haram ya zama ma’aikacin tsaro a gidan kurkuku, wanda aiki ne gwamnatin tarayya ke ɗauka.

Ranar 18 Ga Fabrairun da ya wuce ne balli ya tashi a Sabon Gidan Kurkukun Yola a Jihar Adamawa, inda aka gano cewa a cikin sabbin ma’aikatan kurkukun, har da wani gwanin iya harbi da sarrafa manyan bindigogi mai suna Wilberforce Yohanna.

Hankalin manyan jami’an kurkukun ya tashi da su ka gano cewa Yohanna tsohon ɗan Boko Haram ne.

Wasu sahihan bayanan sirri da Hukumar Kula da Gidajen Kurkuku ta rubuta dangane da Yohanna, sun faɗo hannun PREMIUM TIMES, wadda bayan ta tabbatar da lamarin, buga labarin ya zama wajibi.

Yadda Aka Gano Yohanna Tsohon Ɗan Boko Haram Ne:

An gano Yohanna tsohon ɗan Boko Haram ne tun a wurin bada horo ga sabbin-yanka-raken da ake ɗauka, inda aka je koya masu yadda ake sarrafa bindiga ƙarama da babba.

Jami’an bayar da horo sun lura ko a cikin su babu wanda ya kai Yohanna iya sarrafa bindiga ƙarama ko babba. Iya loda harsasai da hanzari a cikin ƙwarewa, ba a fi shi iyawa ba, sai dai ya koyar, amma ba a koya masa ba.

Yohanna ya zama abin kallo ga jami’an bayar da horo ganin yadda ya ke yi wa bindiga filla-filla, ya kuma haɗa ta a cikin ƙwarewa. Tun a wajen riƙe bindiga babba da ƙarama aka fahimci Yohanna da wani gogarma ne.

An tafi da shi wajen masu bincike, inda bayan an sheƙa masa ruwan tambayoyi, sai ya faɗa masu cewa a gaskiya shi fa tsohon ɗan Boko Haram ne.

Yohanna ya shaida masu cewa amma shi ba aƙidar Boko Haram ya ke da ita ba. Ya yi iƙirarin cewa kama shi ‘yan Boko Haram su ka yi, su ka kuma tilasta shi ɗaukar makami ya taya su yaƙin tsawon shekaru biyu. Daga baya ne ya ya samu wata dama da sa’a, ya tsere, ya kuɓuta daga hannun su. A cewar sa fa.

Sai dai kuma ba a tantance ba shin bayanin yadda ya shiga Boko Haram ɗin da ya yi gaskiya ne, ko kuma ya danne gaskiyar, ƙarya kawai ya yi?

An ɗauki Yonanna aikin kula da kurkuku watanni biyar kafin Boko Haram su kai wa Kurkukun Kuje mummunan harin da har su ka kuɓutar da ‘yan uwan su 64 da kuma haddasa arcewar ɗaurarru fiye da 400.

Majiya daga kurkukun ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa lamarin Yohanna ya zame wa Hukumar Kula da Kurkukun Najeriya alaƙaƙai. Ga shi dai an samu tantagaryar ɗan Boko Haram a cikin su, amma ba a son ɗaga murya don kada ‘yan jarida su yi labari su watsa duniya.

Binciken da PREMIUM TIMES ta yi a cikin jami’an da su ka nemi a ɓoye sunan su, sun tabbatar da cewa, irin birkitaccen tsarin da ake bi idan za a ɗauki sabbin jami’an kurkuku, lalataccen tsari ne, wanda kuɗi kawai mai neman aiki zai biya a ɗauke shi aikin.

“Ba a maganar cancanta, kawai iyar kuɗin ka iyar shagalin ka. Wanda za a ɗauka a matakin Level 8 na ma’aikacin gwamnatin tarayya, zai biya naira 800,000. Matakai na zuwa na ƙasa kuwa a kan biya naira 400,000 ko sama da haka.” Inji wata majiya da ta ce shi ya sa mai laifi ba zai yi wahalar samun shiga aikin jami’an tsaron kurkuku a Najeriya ba.

Idan ba a manta ba, tsohon Gwamnan Jihar Yobe, Sanata Ibrahim Geidam ne ya bijiro da ƙudirin yafe wa tubabbun Boko Haram, a Majalisar Dattawa, kuma aka amince har ƙudirin ya zama doka cikin 2020.

Bayan ƙudirin ya zama doka, an kafa Hukumar Yi Wa Tubabbun Boko Haram Wankin Kankarar Mummunar Aƙida, Koya Masu Sana’o’i da Maida Su Cikin Jama’a.

Sai dai kuma mutane da dama sun riƙa kushe wannan shiri, su na cewa wasu ba tuba su ke yi ba, su na komawa daji wurin Boko Haram duk su kwashi bayanan sirri su kai wa kwamandojin Boko Haram.

Yayin da al’ummar da tubabbun ‘yan Boko Haram ɗin su ka fito cikin su ke ƙyamar sake zama tare da su, Gwamna Babagana Zulum na Barno ya taɓa cewa shirin tarairayar tubabbun ‘yan Boko Haram ɗin ba shi da fa’ida, domin wasun su daji su ke komawa su sake ɗaukar makami.

Sannan kuma za a iya tunawa a ranar Alhamis ce Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya yi iƙirarin cewa shi ya na ganin da haɗin bakin wasu jami’an kurkuku Boko Haram su ka fasa kurkukun Kuje.

PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Kakakin Yaɗa Labaran Hukumar Kula da Kurkukun Najeriya, Abubakar Umar, wanda ya ce labarin ɗaukar tsohon ɗan Boko Haram aikin tsaron kurkuku ba gaskiya ba ne, ƙarya ce.

Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta gano cewa shi ma ɗin bai faɗi gaskiya ba, domin labarin ɗaukar Yohanna aiki ya bazu sosai a cikin manya da ƙananan jami’an Hukumar Kula da Gidajen Kurkukun Najeriya.

Tags: AbujaHausaKurkukuNewsPREMIUM TIMES
Previous Post

Kungiyar NUPENG ta yi wa Ƙungiyar Ƙwadago mubaya’ar shiga zanga-zanga saboda rufe jami’o’i

Next Post

TATTAUNAWA: Budurwar gefe na dauke wa namiji tunane-tunane. Lalacewa ne mai aure ya ajiye budurwar gefe – Inji Mazajen aure a Zaria

Next Post
Man and Woman

TATTAUNAWA: Budurwar gefe na dauke wa namiji tunane-tunane. Lalacewa ne mai aure ya ajiye budurwar gefe - Inji Mazajen aure a Zaria

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Paparoma bai hana ni karɓar mukamin darektan kamfen ɗin Tinubu ba – Lalong
  • Ƴan sanda sun kama wata tsohuwa da ta yi garkuwa da Almajirai uku a Borno
  • Kotu ta yanke wa ɗan shekara 40 hukuncin zaman kurkuku na shekara 16 bisa zargin kokarin aikata fyade
  • Yadda satar ɗanyen mai, fasa bututu da rashin haƙo wadatacce ke hana Najeriya amfanar tsadar fetur a duniya -NESG
  • Duk da ƙalubalen da mu ke fuskanta, Najeriya za ta ci gaba da zama ƙasa ɗaya dunƙulalliya – Buhari

Abinda masu karatu ke fadi

  • Google on Masarautar Kano: Hassada Ta Sa Wasu Na Neman Wofintar Da Kokarin Su Danfodiyo! Daga Imam Murtadha Gusau
  • Kuşburnu Çekirdek Yağı on Dalilin da ya sa muka yi sallar Idi ranar Laraba a Bauchi, muka ki bin sanarwar Sarkin musulmi – Sheikh Dahiru Bauchi
  • Google on HARKALLAR BILIYAN 3.6: Ba nine Balan da ke jerin sunayen masu mallakin kamfanin Adda ba – Gwamna Bala
  • Google on SIYASAR ZAMFARA : Maitaimakawa tsohon dan takarar gwamna a APC akan harkar jarida ya sauya sheka
  • Google on RAMIN MUGUNTA: Yadda Boko Haram suka afkawa bam din da suka dana wa Sojojin Najeriya

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2022 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.