Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin PDP, Atiku Abubakar, ya ƙalubalanci Bola Tinubu ɗan takarar shugaban ƙasa na APC da cewa ya ‘yan jarida su yi doguwar tattaunawa ta sa’a ɗaya cur da shi babu hutawa, kamar yadda Atiku ɗin ya yi.
Atiku ya maida raddin ne bayan Tawagar Kamfen ɗin Tinubu a ranar Asabar ya ragargaji Atiku, bisa dalilin wasu batutuwa da Atiku ya yi magana a kan su a cikin tattaunawar da Gidan Talbijin na Arise TV a Abuja.
A cikin hira da Atiku a ranar Juma’a, 2023: Atiku ya yarfa wa APC shaguɓe kan takarar Muslim-Muslim.
Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ba daidai ba ne da jam’iyyar APC ta tsayar da ‘yan takarar shugaban ƙasa da mataimakin sa duk Musulmai a zaɓen 2023.
Ya ce ya yi mamakin da APC za ta zaɓi wannan baibawan-burmin siyasa, a ƙasa kamar Najeriya mai mabiya addinai da al’adu ba ɗaya ba.
Haka Wazirin Adamawa ya bayyana a tattaunawa da Gidan Talabijin na Arise TV ta yi shi a ranar Juma’a.
A ranar 10 Ga Yuli ne Bola Tinubu ya bayyana sunan tsohon Gwamnan Jihar Barno, Kashim Shettima a matsayin mataimakin takarar sa.
Tinubu da Shettima duk Musulmai ne, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a fagen siyasar Najeriya.
Atiku ya ce batun tikikin Muslim-Muslim shi ne kusan kandagarkin da ya yi masa katanga da Tinubu, shekaru da daɗewa tun ma kafin kafa APC.
Atiku ya bayyana yadda ya ƙi goyon bayan a yi tikitin ‘Muslim-Muslim’, lokacin da zaɓen 20215 ya zo.
“Ni ban yarda a ce daidai ne a ƙasa kamar Najeriya mai ƙabilu da addinai mabambanta, amma a ce wai a fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa duk Musulmai.” Inji Atiku.
Atiku ya ce duk da cewa ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na APC wato Shettima a yankin Arewa maso Gabas ya ke, inda Atiku ya fito, duk da haka Atiku ya ce shi ne ya fi alamun yin nasara a zaɓen shugaban ƙasa da za a yi cikin 2023.
Duk da Atiku ya ce Tinubu abokin sa ne, ya ƙara da cewa hakan bai hana ra’ayin su ya bambanta a fagen siyasa.
Idan ba a manta ba, Shettima ya shaida wa Buhsri cewa Gwamnonin APC Zulum su ka so ya zama mataimakin takarar Tinubu.
Mataimakin takarar Bola Tinubu a jam’iyyar APC, Kashim Shettima, ya shaida wa Shugaba Muhammadu Buhari cewa Gwamnonin Najeriya na ƙarƙashin APC sun so a bai wa Gwamna Babagana Zulum takarar mataimakin shugaban ƙasa.
Shettima ya shaida wa Buhari haka, jim kaɗan bayan da Tinubu ya ƙaddamar da shi a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Shettima ya je Fadar shugaban Kasa ne domin nuna godiya bisa goyon bayan da aka ba shi har aka tsayar da shi mataimakin takarar shugaban ƙasa.
Shettima wanda ya kai ziyarar tare da Gwamna Zulum da Ƙaramin Ministan Gona, Shareku, ya shaida wa Buhari irin yadda gwamnonin APC su ka riƙa matsa wa Zulum lallai ya amince a tsayar da shi mataimakin takara, amma ya ce a’a.
Daga nan ya jinjina wa Zulum sosai ganin yadda ya zaɓi ci gaba da mulki a jihar Barno, maimakon ya tafi takarar mataimakin shugaban ƙasa.
Kafin nan dai Shettima ya jinjina wa Buhari tare da yi masa godiya kan irin ayyukan raya jiha da jihar Barno ta samu a zamanin mulkin APC.
Shugaba Buhari shi ma ya ce “zaɓen Kashim Shettima a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa abu ne mai kyau ƙwarai, saboda ya cancanta.
Ya ce Shettima ya yi Gwamna shekara takwas, kuma ya na sanata, duk tsawon shekarun kuma ya na taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa APC.
Buhari ya ƙara jinjina wa Shettima, ganin duk da cewa a yanzu ba shi ne Gwamna ba, amma bai yada mutanen karkara da jihar sa baki ɗaya, kuma ya na tare da gwamnan da ya gaje shi.
Buhari ya jaddada wa Shettima cewa APC ce za ta yi nasara a zaɓen 2023, kuma kai da Tinubu zan miƙa wa mulki.
“Sai dai kuma maganganu na yabo da ka yi min, zan ƙyale ka, ba zan ba ka amsa har ranar da na miƙa maku mulki kai da ogan ka Tinubu tukunna.” Inji Buhari.
Ƙalubalen Atiku Ga Tinubu: “Mu na yi wa Tinubu ƙalubalen gayyatar da ya je a yi masa intabiyu ta tsawon awa ɗaya, kamar yadda Atiku ya yi ba hutaw. Sai idan ya koro bayanai tiryan-tiryan ba tangarɗa, ba sakin layi a matsayin sa na ɗan takarar shugaban ƙasa, sannan ya ke da baƙin da zai fito ya yi magana.”
Ofishin kamfen ɗin TInubu dai ya zargi Atiku da azurta kan sa ta hanyar wawurar dukiyar ƙasar nan, lokacin da ya ke cikin gwamnati.
Sanarwar Daraktan Kamfen na Tinubu, Bayo Onanuga, ta kuma zargi Atiku da munaficci, watsa ƙarerayi da kuma tantagaryar jahilcin rashin tarihi da kuma rashin sanin abubuwan da ke faruwa yau da kullum.
Sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Atiku, Paul Ibe ya fitar a ranar Asabar, ya ƙalubalanci Tinubu ya fito ya yi intabiyu ta tsawon awa ɗaya ya na magana ba tangarɗa ba sakin-hanya.
“Sai Tinubu ya fito ya yi juriyar da Atiku ya yi sannan ‘yan koren sa za su samu bakin magana.” Inji sanarwar.