Ƴan bindiga sun sace ƴan sanda dake karkashin jihar Nasarawa a jihar Kogi ranar Lahadin da ta gabata.
Ƴan sandan faɗa tarkon ƴanbbindigan ne a hanyar dawowar su daga jihar Osun bayan kammala zaɓen gwamnan jihar da aka yi ranar Asabar.
A tura ƴan sandan jihar Osun domin tabbatar da anyi zaɓen gwamnan jihar lafiya.
An bayyana cewa an yi garkuwa da Ƴan sandan ne a garin Obajana dake jihar Kogi.
Ranar Lahadi da misalin karfe 11:05 na safe mun samu sakon wai an ji karar harbin bindiga a titin Obajana dake kusaa ta tashar ajiye manyan motoci, wato PTI, Obajana.
” Daga nan sai DPO din wannan ofishin ya tura jami’ai wannan wuri. Da suka isa wurin sai suka iske wata mota kirar Bus mai ɗaukar fasinja 18 da wani direba a ciki mai suna Usman Abdullahi da wasu mutum 6 a ciki.
” Mutum 7 din da ke xikin motar dukkan su ƴan sanda ne daga jihar Nasarawa da aka tura aikin zaɓe a jihar Osun.
” Sun bayyana cewa motar su ce ta lalace sai suka tsaya su gyara. A daidai suna haka ne fa kwatsam sai suka ji an diran musu da bindigogi aka sace ƴan sanda 10.
DPOn ya kara da cewa tuni sun aika da dakaru domin bin sahun waɗannan ƴan bindigan da suka sace waɗannan matafiya.
Discussion about this post