Dan takarar mataimakin shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Kashim Shettima ya kalubalanci wadanda suka yi wa kalaman da yayi a hirarsa da talbijin din Channels mummunar fassara cewa su koma su sake kallon hirar, domin ba abinda ya fadi bane ake yadawa, an yi wa kalaman sa mummunar fassara.
Idan ba a manta ba, Sanata Kashim Shettima ya yi hira da Talbijin din Channels inda ya bayyana cewa gwamnatin su na APC idan suka dare kujerar mulki za su yi mulki ne da adalci.
Sai dai kuma wasu kafafen yada labarai sun yi wa kalaman Shettima munanan fassara da ya sa dole ya fito domin ya warware zare da abawa ya bayyana wa ‘yan Najeriya ainihin abinda ya fadi ba kamar yadda ake yadawa ba.
Karanta Sakon Shettima
Na samu saƙonni da dama kan wani rubutu da yake yawo a social media da ake cewa wai na ce ba zan taimaki Musulunci ba idan na zama mataimakin shugaban ƙasar Najeriya.
Da alama wanda yayi wancan rubutu yana da wata mummunar manufa ko kuma yana da ƙarancin fahimtar harshen Turanci da aka yi waccan hirar da shi, da kuma muhallin ita wannan maganar da na yi.
Abinda na faɗa a waccan hira da na yi da Channels TV yayi daidai da matsayar addinin Musulunci akan shugabanci, kamar yadda malaman addini suka sani. Ko a tsarin Musulunci shugaba shi na kowa ne, kuma ana sa ran ya yiwa kowa da kowa adalci ba tare da cutar da wani ɓangare ba.
Yahudawa da Nasara sun zauna a ƙarƙashin mulkin Musulmi tun zamanin Annabi Muhammad (SAW) kuma cikin aminci ba tare da cutarwa ba. Wannan shi ne abinda Musulunci ya koyar da mu.
Haka kuma a matsayina na Musulmi ba zan taɓa amincewa da abinda zai cutar da addini na ba koda ina cikin gwamnati ko bana ciki.
Idan kuma ina cikin gwamnati dole in tabbatar da na kare mutuncin kowa tare da tabbatar da cewa ba a yiwa kowane ɗan ƙasa rashin adalci ko cutarwa ba. Don haka ba zan zuba ido a zalunci addini na ba, ko kuma a Zulunci wani mutum saboda addininsa. Wannan ita ce koyarwar addini, kuma ita ce matsaya ta.
Ga duk wanda yake so zai iya kallon bidiyon hirar da na yi da Channels TV don tabbatar da cewa wancan rubuta da aka yi bai yi daidai da abinda na faɗa ba.
Sanata Kashim Shettima
Mataimakin dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC
Discussion about this post