Sanatan dake wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar Dattawa, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa karkashin sa a majalisar Dattawa ya samarwa Ƴan Kaduna mutum 6000 bashin CBN.
” Mutum akalla 6000 ne muka sama wa bashin Babban Bankin Najeriya ƴan jihar Kaduna. Kuma dukkan su sun ji alat. Wannan bai tsaya nan ba, da zarar an samu karin kuɗi na irin waɗannan basuka zamu ɗibi wasu suma su mori wannan bashi.
Sanata Uba ya kara da cewa jihar Kaduna ce ta biyu cikin jihohin da suka samu bashi mai yawa.
” Baya ga jihar Legas da tafi samun wannan bashi, jihar Kaduna ce ta biyu da ta ragargaji bashin Babban Bankin da akalla mutum 6000 da suka ci moriyar abin, kuma ban tsaya nan ba. Da zarar dama ta samu zamu cigaba.
Idan ba a manta ba Sanata Uba Sani ne jam’iyyar APC ta jihar Kaduna ta tsaida ɗan takarar gwamnan jihar.
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yaba wa zaɓin Uba Sani, ya ce sanatan zai yi aiki don cigaban jihar da mutanen ta.
Mutanen Kaduna da suka tattauna da PREMIUM TIMES HAUSA a garin Kaduna sun yaba wa kokarin da sanatan yake yi wajen taimakon mutanen Kaduna.
Discussion about this post