Gwamnatin jihar Kaduna ta bada hutun kwana biyu saboda mutanen jiha su garzaya ofisoshin zaɓe su yi katin zaɓe.
Hakan na kunshe ne a wata takarda wanda babban mai bashi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye ya fitar ranar Talata.
” Gwamnatin Kaduna ta bada hutun kwanaki biyu, ranar Laraba da Alhamis domin waɗanda ba su da katin zaɓe su garzaya ofishin INEC su yi.
” Haka kuma gwamnatin ta umarci masu kamfanoni da su ɗaga wa ma’aikatan su kafa suma su je su yi katin zaɓen.
Dama kuma idan ba a manta ba a jihar Kaduna ranar Juma’a hutu ce, saboda haka duk mai bukatar sabonta katin zaɓe ga dama ta samu.
A cikin sanarwar, gwamnati ta umarci mutane da su tabbata sun killace katunan su na zaɓe domin da shine za su samu damar kaɗa kuri’a idan zaɓr ya zo.
Discussion about this post