Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a NNPP, Isaac Idahosa, ya bayyana cewa irin gogewa da ƙwarewar sa wajen iya mu’amala da mutane daban-daban a coci, za ta yi wa tafiyar Kwankwasiyya tasiri wajen zaɓen 2023 da kuma bayan zaɓe idan jam’iyyar su ta yi nasara a zaɓen.
Idahosa, wanda ɗan asalin Jihar Edo ne, ya na da mabiya masu ɗimbin yawa, kuma ya shafe shekaru 33 ya na fasto.
A tattaunawar da gidan Talbijin na Channels ya yi da shi a ranar Talata, Idahosa ya ce, “irin gogewa da ƙwarewa ta wajen mu’amala da jama’a ƙabilu daban-daban a coci, hakan zai yi min da kuma yi wa jam’iyyar NNPP tasiri a zaɓen 2023.
“A shekaru 33 da na yi ina fasto. Ina mu’amala da mutane ƙabilu daban-daban, kama daga Hausawa, Yarabawa, Igbo da sauran ƙabilu masu yawa.
“Kuma manyan ‘yan siyasa da ke zuwa ibada coci na, su kan same ni da bayanan matsalolin su da dama, waɗanda su ke neman a magance masu.
“To ka ga idan na yi amfani da irin wannan gogewa, za a samu tasiri sosai.”
Idahosa na waɗannan kalamai ne saboda an ƙalubalance shi cewa bai taɓa shiga fagen siyasa ba, sai wannan lokacin.
Ya ce shi kan sa hulɗa da jama’a a coci a wata siyasa ce mai zaman kan ta.
Ya yi bayanin yadda NNPP za ta magance matsalar tsaro da kuma matsalar taɓarɓarewar ilimi, musamman yajin aikin Malaman Jami’o’i, abin da ya ce yaudarar da gwamnati ke sawa a batun sasantawa ce ta ƙara ruruta wutar yajin aikin.
“Don an biya wa ASUU buƙatun su, ai ba wata bajinta ba ce, tunda haƙƙin su ne.” Inji shi.