Wasu shugabannin Kiristocin jam’iyyar APC sun bayyana cewa sun yi fatali da fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa Musulmi da kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa Musulmi da APC ta yi.
Bola Ahmed Tinubu ne ɗan takarar APC kuma Musulmi ne daga Jihar Legas, kudancin Najeriya.
A ƙarshen makon jiya ne Tinubu ya naɗa Sanata Kashim Shettima ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa, wanda shi ma Musulmi ne daga Jihar Barno, Arewacin Najeriya.
Yayin da ake ci gaba da bayyana ra’ayi mabambanta tun bayan bayyana sunan Shettima da Tinubu ya yi a Daura, a ranar Lahadi, waɗannan shugabannin APC Kiristoci sun ce fitar da Tinubu da Kashim da APC ta yi, tsagwaron rashin kaifin tunanin yakamata ne da rashin adalci a tsarin zamantakewar Najeriya mabambanta addinai da ƙabilu.
Haka kuma wannan ƙungiyar ba’arin Kiristocin APC ta ce tantagaryar rashin adalci ne APC ta yi wa Coci da ɗaukacin miliyoyin Kiristocin da ke ibada a coci a faɗin ƙasar nan.
Sannan kuma sun ce fitar da Tinubu da Kashim Shettima cin amanar haɗin kan zamantakewar al’ummar ƙasar nan ce, wadda kowa ke fatan a ci gaba da dorewar zaman lafiya da juna baki ɗaya.
Hasalallun sun buga misali da yadda wasu manyan malamai da limamai Musulmi su ka yi gargaɗin cewa “haɗa Musulmi tare da wani Musulmi takarar shugaba da mataimaki a jam’iyya ɗaya, rashin adalci ne, kuma yaudara da cin amana ne.”
Waɗannan bayanai na Kiristocin na ƙunshe ne a cikin wata takardar bayan gudanar da taro da su ka fitar a ranar Talata a Abuja, wadda ke ɗauke da sa hannun Farfesa Doknan Sheni.
A ƙarshen taro na su, wanda a zaman su ka tattauna makomar da ƙasar ka iya tsintar kan ta idan APC ta shiga zaɓe da ‘yan takarar shugaba da mataimakin shugaba duk Musulmai, sun ce su kam ba za su iya komawa a mazaɓun su su yi wa Tinubu da Shettima kamfen a zaɓe su ba, saboda dukkan su Musulmai ne.
Sun yi tsokaci cewa Najeriya ƙasa ce ƙasa ce mai mabambantan addinai da ke bin tsarin dimokraɗiyya, ba tsarin addini ba.
Sun ce amma duk da haka, ƙasar na kan wani tafarki ne wanda addini tamkar idanu ya ke ga mulkin Najeriya, domin duk wanda aka tsone, to sai idon ya zubar da ruwa ko hawaye.
A kan haka ya ce duk addinin da aka taɓa a siyasance, to tamkar an taɓo zamantakewar al’umma ne cuɗanye da juna aka taɓa.
Sun ƙara da cewa masu buga misali da 1993 lokacin da aka zaɓi MKO Abiola da Babagana Kingibe, to su sani cewa Najeriyar 2022 fa ba Najeriyar 1993 ba ce. “Sannan kuma ai Abiola da Kingibe ba su yi mulki ko da na minti ɗaya ba. Wato ba a taɓa yin Shugaba Abiola ko Mataimakin Shugaban Ƙasa Kingibe ba.”
Kiristocin sun ce an daɗe ana yi wa APC zargin cewa an ɗora mulkin ta ne bisa turbar da za a Musuluntar da Najeriya, “don haka tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa Musulmi da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa shi ma Musulmi, hakan na nuna cewa biri ya yi kama da mutum.”
Sun kuma yi tir da APC, ganin yadda ta watsar da ta watsar da ‘yan takara Musulmi a cikin kwandon shara.
Sannan kuma ta ƙalubalanci cewa shin a yanzu tunda Shugaban APC ɗan Arewa ne, Mataimakin Shugaban APC ɗan Arewa ne, Shugaban Majalisar Dattawa ɗan Arewa ne, kuma ga Tinubu da Kashim duk Musulmai. “Shin kyamarar za a iya yarda a bai wa Kiristoci irin waɗannan muƙamai a lokaci guda kuwa?”
Idan ba a manta ba, Sanatan da ya falla wa wata mata mari a kantin sayar da kayan ƙarfin maza da mata, ya ce a matsayin sa na Kirista kuma Sanata ɗan APC, ba zai zaɓi Tinubu da Shettima ba, kuma ba zai yi masu kamfen a zaɓe su ba.