Ƴan bindiga sun saki wasu saga cikin fasinjojin da suka tsare hannun sa ranar Litinin da yamma.
Barrister Hassan wanda aka yi garkuwa da shi da matarsa a wannan hari ya isa gidan sa lafiya, kamar yadda matarsa wacce aka saki a cikin farkon wannan wata ta shaida wa PREMIUM TIMES.
Idan ba a manta ba ƴan bindiga sun saki bidiyo dake nuna yadda ake jibgar fasinjojin ranar Lahadi.
Wannan bidiyo ya tada wa mutane da dama hankali.
Fasinjojin sun shafe kwanaki sama da 120 tsare hannun ƴan bindigan.
Rohatanni sun bayyana cewa mutum uku ne aka saki a yau Litinin.
Discussion about this post