Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Atiku Abubakar ya bayyana cewa za a warware matsaloli da dukkan ƙorafe-ƙorafen da su ka bijiro a cikin jam’iyyar.
Korafe-ƙorafen dai sun bijiro ne tun bayan da Atiku ya bayyana sunan Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta a matsayin ɗan takarar mataimakin sa.
A ranar Alhamis ce tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose ya yi wa Atiku wankin babban bargo, inda ya ce ya ci amanar Gwamna Wike, inda ya ɗauki Gwamna Okowa a matsayin ɗan takarar mataimaki, bayan ya yi wa Wike alƙawarin cewa shi zai naɗa.
Shi ma Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya ce Atiku ya baɗa masu ƙasa a ido, ta yadda ya ɗauki Gwamna Ifeanyi Okowa maimakon Wike wanda kwamitin da Ortom ɗin ya jagoranta ya bada shawarar a shi za a ɗauka takarar mataimaki.
Atiku dai na ci gaba da shan suka da caccakar da lamarin ba zai yi wa PDP daɗi ba.
Sai dai kuma wata sanarwa da Atiku ɗin ya fitar a shafin sa na Twitter, ya ce ya na sane da ƙorafe-ƙorafen da ake yi, kuma za a shawo kan lamarin da da daɗewa ba.
“Haɗin kan jam’iyya shi ne matakin farko a ƙoƙarin haɗa kan ƙasa. Daga nan sai haɗa kan jama’a, sai kuma haɗa kan al’ummar ƙasa baki ɗaya.” Inji Atiku.
Ko a yanzu Atiku na shan ragargaza, ganin yadda ya lula Dubai ya yi zaman sa, alhali ga zaɓen gwamnan jihar Osun ya na tafe, ya ƙi zuwa ya yi wa PDP kamfen.
Wannan jarida ta buga labarin cewa Fayose ya yi iƙirarin Atiku ya ci amanar Wike, don haka ba zai goyi bayan kamfen ɗin sa ba -Fayose
Discussion about this post