Yayin da matsalar tsaro ke ƙara muni, rahotanni sun nuna cewa an kashe ‘yan sanda 65, sojoji 85 tsakanin Janairu zuwa Yuni, 2022.
Baya ga wannan adadin, rahotannin sun kuma tabbatar an kashe sauran ba’arin jami’an tsaro waɗanda ba sosoji da ‘yan sanda ba, har su 92.
Waɗannan adadi ne dai da kafafen yaɗa labarai su ka buga. An tabbatar akwai da dama waɗanda ba a lissafa ba, saboda ba su cikin rahotannin kafafen yaɗa labarai.
Rahoton ya fayyace yawan jami’an tsaron da aka kashe a Kudu maso Gabas, Kudu maso Yamma, Kudu maso Kudu da Arewa ta Tsakiya.
Ya kuma ƙididdige yawan waɗanda aka kashe a Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas.
Yayin da Arewa maso Gabas ke fama da Boko Haram, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya na fama da ‘yan bindiga, Kudu maso Gabas kuma na fama da ‘yan ESN, mayaƙan IPOB masu rajin sai sun kafa ƙasar Biafra.
Rahotanni sun nuna an bindige jami’an tsaro 157, yayin da kuma aka kashe farar hula kimanin 3000 a watannin Janairu, Fabrairu da Maris kaɗai na 2022.
Aƙalla an kashe mutum 35,000 a rikicin Boko Haram daga 2009 zuwa 2022, yayin da sama da mutum miliyan uku su ka rasa muhallin su.
A kan matsalar tsaro, cikin makon jiya ne ‘yan ta’adda su ka kai wa dogaran tsaron Buhari hari, su ka kashe sojoji takwas.
Mahara sun kai wa Dakarun sojojin Bataliya ta 7 ta Dogaran Shugaban Ƙasa hari.
Farmakin ya faru a ranar Juma’a da dare, a yankin Bwari da ke Abuja, har su ka kashe sojoji uku, su ka ji wa takwas rauni.
Biyu daga cikin sojojin da aka kashe ɗin manyan jami’ai ne, Kaftin da Laftanar sauran kuma sojoji ne.
Majiya ta ce niyyar ‘yan ta’addar ita ce su je su yi garkuwa da ɗaliban Makarantar Koyon Aikin Shari’a da ke Bwari. Ana jin ma maharan sun yi sansani ne a dajin yankin Bwari.
Hukumar Sojojin Najeriya ba su ce komai ba kan harin. Shi ma Kakakin Sojoji Onyema Nwachuku bai ɗauki kiran wayar da wakilin mu ya yi masa ba.
Amma majiyar leƙen asiri ta sirri daban-daban sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa gwamnati na sane da za a kai farmakin, domin an ƙara matakan tsaro a birnin.
A ranar Litinin an rufe Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Yankin Kwali kusa da Abuja, bayan da ‘yan ta’adda su ka kai hari cikin wata unguwa kusa da makarantar.
Harin da aka yi wanda aka kai wa Dakarun Shugaban Ƙasa, waɗanda aikin su shi ne kare lafiyar shugaban ƙasa, ya faru bayan makonni biyu da kai wa tawagar rakiyar shugaban ƙasa a Dutsinma, Jihar Katsina.
A ranar ce kuma aka kai wa Kurkukun Kuje hari a Abuja, inda su ka kuɓutar da dakarun su na ta’addanci, da sauran ɗaruruwan ɗaurarru.
Harin ranar Juma’a ya zo kwanaki biyu kafin ‘yan ta’addar jirgin ƙasa su ka nuno bidiyon da su ke dukan fasinjojin da su ka tsare a hanyar Abuja-Kaduna.
Cikin bidiyon har barazana su ka yi cewa za su kamo Shugaba Buhari da Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna.
Tabbas An Kai Wa Dogaran Shugaban Ƙasa Hari -Yahaya Bello:
Gwamna Yahaya Bello ya tabbatar da harin da aka kai wa Dakarun Shugaban Ƙasa a Bwari.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna Bello, mai suna Mohammed Onogu ya fitar, ya ce Gwamna ya yi ta’aziyyar waɗanda su ka rasa rayukan su, kuma ya yi jimamin waɗanda aka ji wa ciwo.
Yahaya Bello ya tabbatar da cewa manyan jami’an sojoji biyun da aka kashe, ‘yan jihar Kogi ne.
Ya bayyana kisan su da cewa rashin imani ne, kuma ya yi ta’aziyya ga iyalan su da su ka haɗa da mahaifin Laftanar Suleiman, Kanar Suleiman Ahmodu Babanawa Mai Ritaya da Kaftin Samuel Atta daga Ibaji.
Bello ya yi wa Rundunar Sojojin Najeriya ta’aziyya da jaje.
Discussion about this post