Wani magidanci mai shekaru 47 mai suna Isah Magaji ya roki kotun shari’a dake Rigasa a jihar Kaduna da ta ba shi izini ya tura ɗansa makarantar almajirai a Zariya idan ya kai shekaru bakwai da haihuwa.
Magaji ya ce wannan shine burinsa domin shima karatun Almajirci yayi.
Ya ce baya so dansa ya yi makarantar boko.
Magaji ya roki alfarmar kotun ne bayan da alkalin kotun Salisu Abubakar-Tureta ya bai wa tsohuwar matar Magaji, Ruqayya Lawal izinin kula da dansu daya mai shekara biyu.
Abubakar-Tureta ya ce Magaji zai rika aikawa Ruqayya naira 6,000 kudin abincin yaron duk wata.
Sannan da zaran dan ya cika shekaru 7 zai koma hannun mahaifinsa.
“Daga nan Magaji zai dauki nauyin ci, Sha da karatun sa.
Ita ko Ruqayya ta ce Naira 10,000 duk wata ne zai ishe ta ciyar da yaron.
Abubakar-Tureta ya yi Kira ga Magaji da kada ya sake maimaita kuskuren da iyayensa suka yi a kansa wajen aika dan sa makarantar Almajirci.
“Ni ma makarantar almajirai na yi amma na je makarantar boko. Sannan ban tura ɗa na makarantar almajirci ba ya je na Arabi ne Kuma ya je na Boko.
“A yanzu haka ɗa na ya sauke Kur’ani
Abubakar-Tureta ya ce suna kira ga gwamnati da kada ta rusa makarantun Almajirai amma ta ingantasu yadda za a rika koyar da darusan boko.
Ya ce addinin musulunci ya hana bara.
Discussion about this post