Asusun kula da al’amuran yara kanana ta majalisar dinkin duniya UNICEF ta yi hasashen cewa nan da shekarar 2050 Najeriya za ta samu yara miliyan 29 da aka yi wa auren wuri.
Asusun ta yi wannan hasashe bisa ga wani rahoto da maitaimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbanjo da Asusun suka gabatar a taron ranar Yara na duniya da aka yi ranar Juma’a.
Rahotan wanda aka yi wa taken ‘yadda talauci ke illata rayuwar Yara kanana a Najeriya’.
Abin da rahoton ya nuna
Rahoton ya nuna cewa zuwa yanzu Najeriya na da yara miliyan 22 da aka yi wa auren wuri.
A Najeriya yawan yaran da ake wa aure kafin su Kai shekara 18 ya ragu daga Kashi 48% zuwa Kashi 43% sannan matan aure masu shekara 15 zuwa 19 da ake yi wa aure kafin su Kai shekara 15 ya ragu daga Kashi 12% zuwa Kashi 8%
Matakan da za su rage yi wa yara aure da wuri a Najeriya
Rahotan ya nuna cewa yin amfani da dokan kare hakkin Yara musamman a jihohin Arewacin Najeriya sannan da kafa dokar hana yi wa yara ‘yan ƙasa da shekara 18 aure za su taimaka wajen rage yawan yaran da ake wa aure da wuri.
Yadda talauci ke shafan yara a Najeriya.
Rahotan ya nuna cewa yara kashi 54% sun rasa abubuwa uku daga cikin hakkin yara bakwai a kasar nan.
Wadannan hakokkin yara sun hada da samun abincin dake inganta garkuwar jiki, kiwon lafiya, ilimi, ruwa Mai tsafta, zama a muhalli. dake da tsafta, samun ingantacen gidan zama da samun labarai.
Rahoton ya nuna cewa yara masu shekaru 16 zuwa 17 sun fi yawan yaran da basu samun wadannan hakokkin fiye da Yara masu shekaru 0 zuwa 5.
Yara da dama na fama da matsalar rashin kudi inda kashi 47.4 daga cikin akwai yara maza Kashi 47.98% da kashi 46.8% na mata dake zama a gidajen dake iya kashe Naira 376.5 a rana.
A jihar Legas yara kashi 6.5% ne ke fama da wannan matsala a jihar Legas sannan yara kashi 91.4 % a jihar Sokoto.
Wakilin UNICEF Peter Hawkins ya yi kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki da su zage damtse wajen ganin sun kubutar da Yara daga talauci musamman yadda matsalar ya fi yi wa yaran dake kauye katutu fiye da na birni.