Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto ya bai wa ‘yan takarar shugaban ƙasa mamaki a lokacin zaɓen fidda gwanin shugaban ƙasa na PDP.
Mamakin kuwa shi ne yadda ya sanar da janyewar da ya yi daga takarar, bayan ya rigaya ya kammala jawabin sa na minti biyar daidai da Kwamitin Tantancewa ya bai wa kowane ɗan takara ya fito ya yi bayani.
To sai dai majiya ta tabbatar da cewa bayan Tambuwal ya kammala jawabin sa ya zauna, bayan wani lokaci kuma sai aka ga ya miƙe tsaye, ya kira wani tsohon gwamna daga Arewa ta Tsakiya, sun nufi wurin Gwamna Bala Mohammed, wanda shi ma ɗan takara ne.
Tambuwal ya shaida masa cewa ya je ne ya sanar da shi cewa ya janye wa Atiku.
Wani jami’in APC da ya halarci taron ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa nan take sai aka ga Gwamna Bala ya gigice, ya ƙura wa Tambuwal da tsohon gwamnan ido kawai.
Bayan Gwamna Bala ya dawo cikin hayyacin sa ne ya tambayi Tambuwal dalilin da ya sa zai janye wa Atiku.
Majiya ta ce Bala ya yi iyakar ƙoƙarin hana Tambuwal goyon bayan Atiku, amma ya ce ai ya rigaya ya yanke shawarar yin haka ɗin.
Daga nan sai su Tambuwal su ka bar inda Gwamna Bala ke zaune, su ka nufi wurin Bukola Saraki, shi ma Tambuwal ya sanar da shi cewa ya janye wa Atiku.
Wanda aka yi abin a idon saya ce Saraki ya yi mamakin Tambuwal, inda nan ta ke ya tunatar da shi alƙawari da yarjejeniyar da su biyun su ka yi idan lamari ya kai intaha, to Tambuwal zai janye wa Saraki.
Jin haka sai Tambuwal ya Tubure ya ce kwata-kwata ba su yi haka da Saraki ba.
Ganau ya ce daga nan Tambuwal ya zarce wurin Shugaban Jam’iyya Iyorchia Ayu, ya sanar da shi janyewar da ya yi zai goyi bayan Atiku. Kuma ya ce masa ya shaida wa Bala da Saraki.
An nuno Ayu ya yi ajiyar-zuciya saboda murna, har ya riƙa tattaɓa bayan Tambuwal.
An ce daga nan aka sanar da Shugaban Kwamitin Zaɓen Fidda-gwani na PDP cewa Tambuwal na da wani muhimmin saƙo da zai sanar kafin a fara kaɗa ƙuri’a.
Nan da nan ya je ya yi sanarwar cewa ya janye kuma ya umarci dukkan magoya bayan sa su zaɓi Atiku.
An dai haƙƙaƙe cewa kafin janyewar sa, Tambuwal ya na da ɗimbin magoya baya daga Sokoto, Kebbi, Zamfara, Katsina, Kaduna, Imo, Taraba, Anambra, Nassarawa, Kogi, Ondo da Benuwai.
Don haka ana ganin ɗaiɗaikun ƙuri’u daga wasu jihohi kawai zai buƙata ya lashe zaɓen.
Yankin Arewa maso Yamma da Tambuwal ya fito ne ya fi saura yawan wakilan zaɓen ‘yan takara, har deliget 193.
Bayan kammala zaɓe, Atiku ya samu 371, Nyesom Wike ya samu 237.
Yadda Tambuwal Ya Shirya Min Tuggu -Wike:
Gwamna Nyesom Wike ya tayar da rigima, da ya hargitsa zaɓen fidda-gwani, kowa ya rasa, saboda maƙarƙashiyar da ya ce an yi masa.
Ya ce a wurin taron zaɓen, ya ga yadda mutum har mutum amma lokaci ɗaya zai rikiɗe ya koma mutum-mutumi.
Gwamna Nyesom Wike ya zargi Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto da wani Gwamnan Kudu maso Kudu da cin amanar sa da kuma shirya masa maƙarƙashiya a wurin zaɓen fidda-gwanin ‘yan takarar shugaban ƙasa, wanda aka yi a ranar Asabar a Abuja.
Wike ya yi wannan kakkausan kalamai ne a Fatakwal, wurin gangamin da aka shirya domin tarbar sa, bayan ya koma gida daga wurin zaɓen fidda-gwanin da ya samu ƙuri’u 237. Atiku Abubakar ne ya kayar da shi, bayan ya samu ƙuri’u 371. Bukola Saraki ya samu ƙuri’u 70, yayin da Gwamna Udom Emmanuel na Akwa Ibom ya samu ƙuri’u 31.
Wike ya yi zafafan kalamai ne sakamakon maƙarƙashiyar da ya ce an shirya masa a wurin taron, yadda shugabannin jam’iyyar PDP su ka bari Tambuwal ya janye daga takara, alhali a lokacin bai kamata ya janye ba, saboda lokacin janyewar ta sa ya wuce.
A bayanin Wike, ya ce Kwamitin Tantance ‘Yan Takara a zalunce shi, domin ya bayar da dama ga Tambuwal ya yi magana sau biyu. Hakan kuma a cewar Wike, an karya ƙa’idar zaɓen fidda-gwani.
“Da na so tayar da fitina, da sai na tashi daga inda na ke na je na ce ban yarda a ci gaba da taron ba. Saboda an bai wa Tambuwal lokacin da ya zarce na kowa, kuma na ƙa’ida, har ya yi dogon jawabin cewa ya janye, ya goyi bayan Atiku Abubakar.
“Amma saboda ba na son tayar da fitinar da za ta hargitsa PDP baki ɗaya, sai na haƙura don a zauna lafiya.
Wike dai ya yi raga-raga da shugabannin PDP, ya ce kwata-kwata babu adalci a lamarin su.
Da ya koma kan Gwamnonin Kudu maso Kudu, Wike ya ce wanda ya ci amanar sa bai rage shi da komai ba, amanar kan sa ya ci.
Bisa alama ya na magana ne kan Gwamna Ifeanyi Okowa na Delta, wanda wakilan zaɓen ‘yan takarar jihar sa su ka zaɓi Atiku, maimakon Wike, kamar yadda shi Okowa ɗin ya sha cewa ɗan Kudu za su zaɓa.
“Na taya Atiku murna don a tafi tare, kuma jam’iyya ta kauce wa ruɗani. Na sanar da shi da ya zo gida na a Abuja cewa na ga wasu tarkacen gwamnoni da ‘yan miya-ta-yi-zaƙi na bin ka ɗuuu. To waɗannan duk fanko ne, ba su da mutane. Ni ke da mutane, kuma ta tabbatar zaɓe ya nuna haƙa.”
Masu nazarin siyasa na ganin cewa magoya bayan Tambuwal da na Gwamnan Delta ne su ka ƙara wa Atiku yawan ƙuri’u, har ya kayar da Wike.”
Gwamna Wike ya ce tunda Kudu ba su da haɗin kai, daga yau kada wani maras kunya ya fito ya ce Arewa ta danne su, domin su ne su ka danne kan su.
Idan ba a manta ba, Wike ya goyi bayan Tambuwal a zaɓen fidda gwani na ‘yan takarar shugaban ƙasa na PDP.
Discussion about this post