Kakakin Majalisar Tarayya Femi Gbajabiamila ya nuna damuwar sa ganin yadda Mambobin Majalisar Tarayya da Sanatoci da dama su ka kasa cin zaɓen fidda-gwani.
Ya ce ba wani abu ya kayar da su ba, sai tsarin bai wa ‘deliget’, wato wakilan zaɓen ‘yan takara damar zaɓen wanda su ke so.
Gbajabiamila ya ce “yawancin waɗanda su ka kasa cin zaɓen fidda-gwani ba al’ummar da su ke wakilta ne ba su son su ba. Kawai dai wakilan zaɓen ‘yan takara ne, wato ‘deliget’ su ka kayar da su.
“Wannan tsari kuwa shirme ne, shi ya sa mu a Majalisar Tarayya mu ka yarda a bi tsarin ‘yar tinƙe kawai wajen zaɓen fidda gwani.” Inji Gbajabiamila.
Ya ce rashin ci gaban mambobin a zauren majalisa wanda za a kafa a 2023, babbar asara ce ga ƙasa, talakawa da dimokraɗiyya ɗungurugum.
A tsawon watanni biyu da aka shafe har zuwa bayan kammala zaɓukan ‘yan takara, an ga yadda aka riƙa yin watandar kuɗaɗe ga ‘deliget’, wanda a tarihin zaɓukan Najeriya na baya ba a taɓa ganin hauka da kuma ɓarusa da watandar kuɗaɗe ba wajen zaɓen fidda gwani kamar na cikin 2022.
Gbajabiamila ya yi kira ga ‘yan majalisar tarayya waɗanda ba za su sake tsayawa takara ba, su ci gaba da sadaukar da kan su wajen kare dimokraɗiyya a wannan sauran shekara ɗaya da ta rage masu.
Idan ba a manta ba, cikin waɗanda su ka sha kaye a zaɓen fidda gwani, har da Honorabul Fatuhu, ɗan uwan Shugaba Muhammadu Buhari, kuma mai wakiltar Mazaɓar Buhari a Daura.
Bayan ya sha kaye, ya yi zargin cewa murɗiya aka yi masa, kuma zai nemi haƙƙin sa a kotu.
Daga nan kuma ya ce idan aka ƙi yi masa adalci, to ya yi rantsuwar cewa sai ya tarwatsa APC a Jihar Katsina.
Fatuhu dai ya yi barazanar komawa jam’iyyar NNPP mai kayan marmari, kamar yadda za ku sake karantawa a ƙasa.
Ɗan’uwan Buhari Ya Yi Rantsuwar Tarwatsa APC:
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙananan Hukumomin Sandamu/Daura/Mai’aduwa, Fatuhu Muhammad, ya yi barazanar tarwatsa jam’iyyar su APC, a Jihar Katsina.
Fatuhu wanda Shugaba Muhammadu Buhari kawun sa ne, kuma sun yi kama da juna sosai, ya yi barazanar komawa jam’iyyar NNPP, sakamakon abin da ya kira rashin adalcin da ya ce an yi masa wajen kifar da shi a zaɓen fidda gwani.
Wani mai suna Aminu Jamo ne ya kayar da Fatuhu da ƙuri’u 117, shi kuma Fatuhu ya samu ƙuri’u 30 kacal.
A cikin wata magana da Fatuhu ya yi ta waya, shi da wani kuma aka riƙa watsa rikodin ɗin maganar, Ɗan Majalisar ya yi iƙirarin cewa fashi aka yi masa, kuma sai ya ƙwato haƙƙin sa, ko kuma ya fice daga jam’iyyar.
Hirar wadda ke da tsawon minti 6 da sakan 22, PREMIUM TIMES ta saurari inda Fatuhu ke magana da wani da ya ke kira Ranka Ya Daɗe, ya na ce masa sai ya tarwatsa APC a Jihar Katsina.
Ya ce shi ba zai tsaya sake wani zaɓen fidda gwani ba, ko ma da jam’iyya ta ce a sake ɗin. Saboda shi ne wanda ya lashe zaɓen fidda gwanin da aka yi, amma aka danne masa.
“Ba za su iya sake wani zaɓe ba. Saboda ni na yi nasara a zaɓen farko da aka yi. Sun karya doka. Don haka a ba ni takara ta. Ko mu haɗu a kotu, ko kuma na tarwatsa APC, na kawo wata jam’iyya a Daura.” Inji shi.
“Zan fa iya rungumo jam’iyyar nan ta Kwankwaso mai kayan marmari na kai ta a Daura.
“Zan iya kai NNPP a Daura, saboda kowa kan sa kawai ya ke so. Su zo su bayyana abun da su ka yi wa talakawa, ni ma na kawo abin da na yi masu, a ga wanda mutane za su bi.” Inji Fatuhu.
Fatuhu ya ce idan ya tashi tsiyar sa, ba a Daura kaɗai garin Shugaba Buhari zai tarwatsa APC ba, har da cikin jihar baki ɗaya.
“Na rantse sai na tarwatsa APC a Jihar Katsina, saboda ɗan takarar NNPP na zaɓen gwamnan Jihar Katsina, Nura Khalil da mutanen sa na jira na.
“Ba zan bari wasu su ƙuntata min ba. Saboda idan da mulkin nan gado ne, ai da ni ne zan gaji Shugaba Buhari, Saboda ni ne ɗan uwan sa na jini.”