Shugaban kas Muhammadu Buhari ya mika sakon taya murna ga ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu bisa nasarar da ya samu a zaɓen fidda gwani.
Tinubu ya yi nasara a zaɓen fidda gwani na APC wanda aka kammala ranar Laraba a Abuja.
A sakon taya murna wanda shugaba Buhari ya aika wa Tinubu ya ce dole dukka wani ɗan APC ya mara wa ɗan takarar baya.
” Yanzu an yi zaɓe an gama. Tinubu ne kuma ɗan takarar mu dole dukkan mu mu zo mu haɗa hannu domin ganin jam’iyyar ta yi nasara a zaɓen shugaban kasa da ke tafe.
” Wakilan mu da suka yi zaɓe sun yi zaɓen da ya da ce. Tinubu shine ɗan takarar da ya dace a zaɓa.
” Muna da yaƙinin cewa Idan Tinubu ya zama shugaban Kasa zai ɗora daga inda muka tsaya. Tattalin arzikin kasa zai bunƙasa, za a samu cigaba a harkar Ilimi da tsaro.
” Irin haɗin kan da muka yi dukkan mu a 2013 muka kafa tarihi wajen cire gwamnati mai ci a zaɓen shugaban kasa shine za mu yi a wannan karon idan muna so mu samu nasara a zaben dake tafe.
” A karshe ina so in godewa wakilan mu da suka zaɓi Tinubu ɗan takarar jam’iyyar mu ta APC. Zaɓen sa da aka yi shine ya fi dacewa kuma mafi alkhairi a garemu.